✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Batanci: Yadda batun Deborah ya fara sauya tunanin mabiya addinai

Annabi (SAW) shi ne martabar addininsu don haka dole a kare mutuncinsa. Kiristanci ba zai taba goyon bayan batanci ga wani addini ba.

Bayan tayar da jijiyar wuya a tsakanin mabiya addinin Musulunci da na Kirista kan kisan dalibar Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da ke Sakkwato, Deborah Samuel bisa zarginta da yin batanci ga Annabi (SAW), alamu sun nuna cewa mabiya addinan biyu sun fara sauya tunaninsu kan yadda suke daukar abubuwa tare da fara nemo hanyar magance tashin hankali a tsakanin mabiya addinan.

A ranar Alhamis din makon jiya ne wadansu matasa da ake zargin daliban kwalejin ne suka kashe tare da kona gawar Deborah wadda ta fito daga yankin Rijau a Jihar Neja, bayan sun zarge ta da yin batancin.

Fadar Sarkin Musulmi ce ta nuna rashin jin dadinta kan faruwar lamarin, inda Majalisar Sarkin Musulmi ta soki batancin da kuma daukar doka a hannu da daliban suka yi suka kashe dalibar.

Gwamnatin Jihar Sakkwato ta rufe makarantar tare da bayar da umarnin a gudanar da cikakken bincike a kan lamarin.

Malamai da shugabannin addinai da fitattun marubuta a jaridu ma sun yi ta suka kan faruwar lamarin tare da nuna gazawar mahukunta wajen magance irin wannan lamari wanda a ganinsu ba yanzu aka fara haduwa da shi ba.

Fitaccen malamin nan na Kano Sheikh Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo ya fitar da wata sanarwa a shafinsa na Facebook ranar Asabar, inda ya jero wasu abubuwa da yake ganin da an bi su za a kauce wa aukuwar irin abin da ya faru a Sakkwato.

Ya ce, “Mun jima muna jan hankalin mahukuntan Najeriya kan a rika gaggauta hukunta masu miyagun laifuffuka a cikin al’umma, amma hakan ya kasa samuwa.”

Ya ce mutane sun fara gajiya da sakacin hukumomi game da hukunta masu laifi, har sun fara ba kansu lasisin daukar doka a hannunsu, wanda ba haka aka so ba.

Shehin Malamin ya ce lokaci ya yi ga wadanda ba Musulmi ba a ko’ina a duniya, su fahimci girman Annabin Rahma a zukatan Musulmi.

“Duk wani Musulmi abin alfahari ne a gare shi ya sadaukar da komai nasa, har ma da rayuwarsa wajen kare martabar Annabin Rahma.

“Don haka, su guji aikata duk wani abu da zai shafi mutuncinsa (SAW) da darajarsa, domin duk sa’ar da wani ya yi haka, to sakamakon ba zai zo da sauki ba,” inji shi.

Dokta Sani Rijiyar Lemo ya ce, “Babban abin da ya dace shi ne, hukuma ta ja kunne da kakkausan harshe a kan duk wanda zai yi tunanin batanci ga wani daga cikin annabawan Allah da kuma daukar mataki mai tsananani a kansa.”

Sai ya yi kira ga al’ummar Musulmi su kwantar da hankali, su guji duk wata fitina da za ta haifar da tashe-tashen hankali da tarzoma.

Shi ma Shugaban Majalisar Malamai ta Kasa ta Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah, Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir, bayan ya yi Allah wadai da kalaman batancin da dalibar ta yi, ya shawarci Musulmi su guji daukar doka a hannunsu domin kada su ba makiya Musulunci da makiya Najeriya damar haddasa fitina da kashe-kashe a kasar nan.

Sheikh Jingir ya ce, batanci ga Annabi (SAW) babban laifi ne, sai dai daukar doka a hannu wajen kashe wadda ta yi batancin, babban kuskure ne da ka iya bayar da kafar da makiya Musulunci da Najeriya za su haddasa fada a tsakanin Musulmi da Kiristoci.

Mataimakin Babban Editan Daily Trust, Suleiman A Suleiman a ranar Litinin a rubutunsa mai kanun “Kurakurai biyu da na uku” ya soki kalaman batancin da kuma daukar doka a hannu da daliban suka yi wajen kashe dalibar da kuma wadanda suka kare tabargazar Deborah, inda ya ce hakan ya nuna rashin girmama abin da Musulmi suka yi imani da shi.

Haka marubucin Daily Trust Tunde Asaju ma a rubutunsa mai kanun: “Kan Deborah Samuel: Kurakurai biyu ba su zama daidai” a ranar Talata ya soki batancin da kuma daukar doka a hannu da daliban suka yi.

Marubutan biyu sun yi dogon bayani tare da bayar da shawarwari kan yadda za a kauce wa aukuwar haka a nan gaba.

Ga alama hakan ya sa a karon farko Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), Dokta Samson Ayokunle, ya sauya salo, inda ya bukaci Kiristoci su rika mutunta addinan sauran abokan zamansu, tare da nanata bukatar su rika kokarin gano abubuwan da mabiya addinan suke so su rika girmama su da wadanda ba su so don su kauce musu.

Dokta Ayokunle ya bayyana haka ne lokacin da yake magana a shirin The Morning Show na gidan Talabijin na Arise a ranar Litinin, inda ya ce ya kamata a koya wa dalibai su rika kai rahoto ga hukumomin da abin ya shafa ko na tsaro idan irin haka ya taso.

Ya ce, “Akwai bukatar a samu ilimin addinai don ku san abin da mabiya wasu addinai da ke kusa da ku ba sa so, kuma ku girmama su.

“Idan aka samu mutunta juna a wannan kasa, za a samu zaman lafiya. Kuma kada ku dauki matakin hukunta duk wanda ya yi muku laifi.

“Ku kai rahoto inda ya kamata. A iyakar sanina ban ga sunan wani malamin addini da aka ambata a cikin dukkan takardun da na samu daga mutanenmu na Sakkwato ba.

“Kashe yarinyar nan da kona gawarta babban abu ne da bai kamata a kara bari ya faru a kowane bangaren addini ba.

“Kuma ina gargadi ga wadansu malaman addini da suke cewa akwai bukatar a kiyaye ketare musu jan layi.

“A kasar da muke da dimokuradiyya, idan akwai layin da bai kamata a tsallaka ba idan aka tsallaka, ku kai rahoto ga hukuma kuma ku bar jami’an tsaro su yi aikinsu a kai.

“Sannan ina kira ga kowane Kirista ya girmama sauran addinan da suke kewaye da ku,” inji shi.

Ayokunle ya ce, babu wanda ke da hakkin daukar doka a hannu balle ya kashe wani mutum, “Idan gwamnati ta gaza daukar kwakkwaran mataki na gurfanar da wadanda suka aikata laifin a gaban kotu don a hukunta su, to za mu sanar da duniya don taimaka wa Kiristocin Najeriya,” inji shi.

Masu sharhi da dama sun nuna wa shugabannin Kiristocin abin da ya kamata su yi idan ana son zaman lafiya a tsakanin mabiya addinai a kasar nan.

Daya daga cikinsu ya ce, “Yayin da muke sukar abin da ’yan uwanmu suka yi na daukar doka a hannu, wajibi ne mu yi kira ga shugabannin Kirista su rika ilimantar da mabiyansu abin da ya dace, domin ba daidai ba ne mabiyin wani addini ya yi batanci ga Annabi ko addinin wasu ba.

“Annabi (SAW) shi ne martabar addininsu don haka dole a kare mutuncinsa.”

Kungiyar Kare Hakkin Musulmi ta MURIC ma yayin da ta soki kisan ta kuma bukaci shugabannin Kirista su ilimantar da mabiyansu kan bukatar su rika girmama addinan sauran jama’a, domin ba addinin Musulunci ne kawai ba, hatta dokokin Turawasun ce batanci ga Annabi ko kowane addini babban laifi ne.

Wani Kirista mai suna Samaila Yunusa Dan-Mairo ya rubuta a shafinsa na facebook cewa, “Debora ta yi kuskure wajen mayar da martani ga abokan karatunta kan aika sakon addini a shafin Wasof na ajinsu ko da ba don haka aka bude shafin ba.”

“Na saurari muryarta a cikin harshen Hausa da ake yadawa a kafafen sadarwar zamani, wajibi ne a la’anci wadannan kalmomi.

“Ba ta yi mu’amala mai kyau da makwabta da abokan karatunta a abin da ya shafi addini ba.

“Kalaman na tunzurawa ne ga mabiya addinin Musulunci da al’ummar Musulmi, hatta Kiristan da yake girmama addinin Musulunci ba zai amince da haka ba.

“A matsayina na Kirista ba zan so dan uwana Kirista ya fadi irin wannan ga dan uwa Musulmin da yake aiki da addinin Musulunci ba,” inji shi.

Bayan ya kawo jawabin nata da Hausa, sai ya ce: “Wadannan kalaman batanci ne da cin zarafin Annabi Muhammad da addinin Musulunci.

“Babu tilastawa a cikin addini, don haka akwai bukatar mu rika girmama fahimtar mutane da tsarin addininsu a duk inda muke zaune.”

Ya yi dogon bayani kan yadda yake zaune lafiya da makwabtansa Musulmi da yadda ya fito daga zuriyar da ta kunshi Musulmi da Kirista sai ya ce: “Babban nauyin da ke kanmu a matsayinmu na kasa shi ne mu fahimci yadda za mu koyar da ’ya’yanmu girmama dan Adam da girmama abin da addinin mutane ke daukarsa da muhimmanci.

“Wannan ce hanyar tabbatar da zaman lafiya.”

Da yake tofa albarkacin bakinsa kan bayanin Samaila Dan-Mairo, Philemon Ephraim cewa ya yi: “Yallabai, ba zan iya sukar makasan ba, ba tare da na soki wadda aka kashe ba a wannan lamari.

“Kuma ban yarda a ce kisan ya dace ba, saboda na ji an ce kisan rai ba tare da bin doka ba, zunubi ne kuma Musulunci ya la’anci haka.

“Ina fata za mu la’anci ayyukan biyu don mu kauce wa abin da zai biyo baya. Domin ina tabbatar maka in da yarinyar ta fito daga yankina ne da batun “Rikicin addini” ne zai mamaye abin da ake tattaunawa a Najeriya a yanzu. Shin muna bukatar haka? Na rantse ba mu so.

“Addinin Kirista bai yarda ba, kuma ba zai taba goyon bayan batanci ga wani addini ba, kamar yadda ba zai taba goyon bayan a dauki doka a hannu ba,” inji shi.