✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Batar Naira Tiriliyan 5: Majalisa ta soma binciken hukumomin 252

Majalisa za ta aika da sammacin tiso keyar duk wata Hukumar da ta ki amsa gayyatar kwamitin.

Kwamitin Kula da Asusun Bukatun Ba-zata na Majalisar Dokokin Tarayya, ya fara binciken kashe Naira tiriliyan 5 da Hukumomi 252 suka yi tsakanin shekarar 2017 zuwa 2021.

Binciken na zuwa ne bayan gano hukumomi da dama na karbar kudade daga Asusun ba tare da sahalewar kwamitin da doka ta ba wa damar sa ido a kai ba da Majalisar Dattawan ta yi.

Da yake ganawa da manema labarai, Shugaban Kwamitin, Sanata Mathewa Urhoghide ya ce “muna so mu ga yadda aka kashe wadannan kudaden ne, saboda akwai rudani akan tsarin fitar da kudin.

Ya kuma ce Majalisar za ta aika da sammacin tiso keyar duk wata Hukumar da ta ki amsa kiran gayyatar kwamitin.

Kazalika, Sanatan ya ce Shirin Ci gaba Mai Dorewa na Gwamnati (SDG) ya samu Naira biliyan 180, sai NBET da ya karbi Naira Biliyan 2.9, yayin da ma’aikatar jin kai ta karbi Naira biliyan 445.

Sauran Hukumomin da za su bayyana gaban kwamitin sun hada da Ma’aikatar Yada Labarai da Al’adu, da ta Tsaro, da ta Shirin Inshorar Lafiya na Gwamnati, da rundunar ’Yan Sanda, da Ma’aikatar Kula da Lantarki ta kasa.

Sauran sun hada da Bankin Ma’aikata, da Ma’aikatar Ba da ruwan sha, da Majalisar Tarayya, da Hukumar Yaki da Cin hancin da Karbar Korafe-Korafe ta kasa hadi da Hukumar Tsaro ta DSS.