✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Batun komawar Yari PDP ya sha ruwa bayan ya sasanta da Matawalle

Sanata Abdullahi Adamu ya yi uwa ya yi makarbiya wajen sulhunta Yari da Matawalle.

Batun komawar tsohon Gwamnan Jihar Zamfara zuwa jam’iyyar adawa ta PDP ya sha ruwan bayan ya yi sulhu da gwamnan jihar mai ci a yanzu.

Shugaban jam’iyyar APC na Kasa, Sanata Abdullahi Adamu ya sasanta tsohon gwamnan Zamfara, AbdulAziz Yari da gwamna mai ci Bello Matawalle.

A wani zama da aka yi ranar Litinin a Abuja, Sanata Adamu ya gana da dukkan bangarorin biyu inda suka tattauna a tsakanin su sannan ya shiga tsakaninsu ya sasanta su.

Idan ba a manta ba a cikin watan Maris shugaban jam’iyyar PDP na Jihar Zamfara ya sanar wa manema labarai cewa Yari da makarraban sa sun sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP.

Sai dai bayan haka Sanata Kabiru Marafa ya sanar cewa an riga malam masallaci ne amma har yanzu basu koma PDP ba.