✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bature ya koma baki bayan shan wani magani

Cikin mako daya sai fatar Monk mai shekara 34 ta fara canja launi.

Wani Ba’amurke farar fata daga Jihar Lousiana da ke Amurka mai suna Tyler Monk launin fatarsa ya koma baki ba sakamakon shan wani maganin hana damuwa da aka rubuta masa.

Jaridar Daily Mail ta ce wani likita ne ya rubuta wa Tyler Monk wani magani mai suna Prozac a watan Mayun bara sakamakon gano yana fama da ciwon damuwa da gajiya.

Cikin mako daya sai fatar Monk mai shekara 34 ta fara canja launi.

Monk, wanda sufeton feshin yaki da kwari ne ya ce ya daina shan maganin bayan makonni kadan – amma fatarsa ta ci gaba da zama baka-baka.

Kunnensa ne ya fara canja launi kafin lamarin ya watsu zuwa wuyarsa da fuskarsa – sai kuma ya mamaye hannu da kafarsa.

Mista Monk ya ce ya kuma hadu da wasu alamun cututtuka da suka hada da jan alama da zafi a ido da yadda yake jin mugun zafin rana a jikinsa da kuma jin tamkar ya kone.

Da farko, Tyler bai yarda abin da mutane ke fadi cewa fatarsa na sauya launin ba lokacin da abokan aikinsa ke labarta masa bayan sun fahimci sauyin a jikinsa.

Sai dai bayan da abokansa da yawa suka fada masa cewa launin fatarsa na sauyawa kuma ya fara gani a jikinsa ne ya fara yarda da lamarin inda ya yanke shawarar zuwa asibiti don a duba lafiyar fatarsa.

Duk da cewa likitocin fata da yawa sun bincika tare da duba fatar tasa sun gaza gano abin da ya haifar da sauyin launin fatar.

Sai dai Tyler ya yi zargin cewa maganin rage damuwa da ya taba sha ne ya yi sanadiyyar hakan duk da likitoci ba su tabbatar da hakan ba.

Bayan yunkurin da likitocin suka yi na gano abin da ke damun fatar tasa ya ci tura ne Tyler ya hakura gaba daya ya rungumi kaddarar da ta fada kansa.

Mutanen da ke bibiyar al’amuran Tyler a TikTok da sauran shafukan sada zumunta da yake amfani da su, sun gano cewa launin fatar tasa ya sauya daga yadda suka san shi a baya.

Wasu daga cikinsu sun taya shi alhinin wannan lamari da ya afka masa inda wasu kuma suka fara zolayarsa da kalmomi daban-daban kan sauyin da ya samu a fatar.

Maganin Fluodetine da ake kira da Prozac, wani maganin ciwon damuwa ne samfurin da aka fi sani da (SSRI).

Tyler Monk

Fiye da Amurkawa miliyan 28 ne suke shan maganin fluodetine. Kuma samfurin SSRI ne mafi shahara a magungunan ciwon damuwa da ke aikin dakile hauhawar damuwa a kwakwalwa.

Kuma ba a cika samun wadannan magunguna su jawo wa fata canjin launi ba.

Matarsa Emily Monk ta ce sun yi bakin kokarinsu su ilimantar da ’ya’yansu mata biyu kan canjin launin fatar ba tare da sun firgita ko sun damu ba.

Misis Monk ta ce: “Ni da ’ya’yan mun fi damuwa da batun lafiyarsa. Ba mu damu da canjin launin fatar ba, matukar lafiyarsa kalau babu damuwa.”

Ta sanya batun a shafon TikTok don wayar da kai a kan wannan magani tare da gargadin saura kan illar da yake iya haifarwa.

Takan tattauna da mutane a sassan duniya ta kafar kan yadda za a yi kan lamarin da ko za su samu taimako.

Kuma ta kaddamar da wani shafi mai suna GoFundMe bisa fatar tara wasu kudi don jinya da tafiye-tafiye da sayen magunguna da jinyar da za a bukata.