✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bayan bude makarantu a Zamfara: Iyaye sun ki tura ’ya’yansu

Dalibai sun ki komawa makarantu domin daukar darasi a Jihar Zamfara, bayan an bude su, bayan wata hudu da rufewa saboda matsalar tsaro.

Dalibai sun ki komawa makarantu domin daukar darasi a Zamfara bayan gwamantin jihar ta sake bude makarantun da ta rufe kimanin wata biyar da suka gabanta.

Kazalika, iyaye sun ki tura ’ya’yansu zuwa makarantun, kamar da wani uba ya shaida wa wakilinmu cewa jira yake sai ya ga irin matakan tsaron da hukumomi za su dauka a makarantun kafin ya sake tura ’ya’yansa.

“’Yata tana cikin wadanda aka sace a Makarantar Sakandaren ’Yan Mata da ke Jangebe a bara, wanda ya sa muka shiga tashin hankali sosai.

“Saboda haka ina jira ne in ga irin matakin tsaro da za a dauka a kan wadannan makarantun sannan zan duba yiwuwar mayar da ’ya’yana makaranta,” inji shi.

A watan Satumban 2021 ne dai Gwamnatin Zamfara ta rufe makarantun firamare da sakandare da manyan makarantun da ke jihar bayan ’yan bindiga sun tsananta kai hare-hare da kuma sace dalibai a makarantun.

’Yan bindigar sun kai wani hari tare yin garkuwa da dalibai kimanin 80 a wata makarantar je-ka-ka-dawo da ke garin Kaya kafin daga bisani a sake so yaran.

A watan Fabarairun bara kuma, an yi garkwua da daruruwan dalibai mata a Makarantar Sakandaren ’Yan Mata ta Gwamnati da ke garin Jangebe a Karamar Hukumar Talata Mafara ta jihar.

Hakan ne ya sa a baya kungiyar maharba ta jihar ta rubuta wa Gwamnan Jihar Zamfara, Muhammad Matawalle, neman gwamnatin ta dauke su aikin kare makarantun jihar.

Maharban sun kuma kuma yi nuni tare da bayar da tabbacin cewa za su tsaya kai da fata wajen kare makarantun.

Gwamnatin Zamfara ta bude makarantu

A ranar Lahadi ne dai Gwmnatin Jihar Zamfara ta sanar da sake bude makarantu 115 da ke jihar, bayan sun kwashe kimanin wata biyar suna rufe.

To sai dai har ya zuwa lokacin kammala hada wannan rohoton, binciken da wakilin ya gudanar ya nuna cewa dalibai ba su koma karatu a galibin makarantun ba.

A wata sanarwa da Ma’akaitar Ilmin Jihar Zamfara ta raba wa manema labarai, gwamnatin jihar ta sanar da cewa makarantun za su fara gabatar da darussa ne daga ranar Litinin 17 ga watan Janairun wannan shekarar.

An raba makarantun gida uku

Kuma an raba makarantun jihar zuwa gida uku koraye, jajaye da kuma launin rawaya .

Korayen makarantun su ne wadanda ake ganin ba su cikin wata barazana, kuma yawancinsu suna a Gusau ne, babban birnin jihar.

Makarantu masu launin rawaya kuma su ne wadanda suke a hedikwatocin kananan hukumomin jihar, amma suna fuskantar barazana, sai dai ba mai yawa ba.

Rukunin biyu masu kunshe da makarantu 115 su ne aka bude a halin yanzu.

Su kuma jajayen makarantu su ne wadanda suke cikin hatsari suke yankunan karkara inda babu cikakaken tsaro.

Su ne guda 80, kuma za su kasance a rufe, har sai yanayin tsaron yankunan da suke ya inganta, a cewar ma’aikatar ilimin.