✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bayan cika baki, minitsa ya kasa gyara wutar lantarki

Bidiyonsa yana caccakar magabatansa kan rashin samar da wutar ta tayar da kura.

Duk da cika bakin da Babatunde Fashola ya yi cewa zai magance matsalar wutar lantarki a Najeriya, tsugune ba ta kare ba, har aka sauke shi, bayan shafe wata 42 da ya yi a matsayin minista.

Bayan nada shi Ministan Lantarki, Ayyuka da Gidaje a 2015, Fashola ya yi wa kamun ludayin magabatansa a bangaren lantarki shagube da cewa ’yan koyo ne; yan bugun gaba tare da ba wa ’yan Najeriya tabbacin cewa yana da kwarewar da zai share musu hawaye a bangaren wutar lantarki.

Amma har zuwa 2019 tsugune ba ta kare ba, inda Shugaba Buhari ya sauke Fasola, wanda lauya ne, ya nada injiya, Sale Mamman a matsayin minista, ya kuma rabe ma’aiktar lantarki daga ragowar ma’aikatun.

Wani bidiyon da ka wallafa a YouTube ya nuna kalaman na Fashola, lokacin yana gab da karashe mulkinsa a matsayin Gwamnan Legas, jim kadan kafin babban zaben 2015, wanda Shugaba Buhari ya lashe.

A bidiyon da tsohon hadimin tsohon Shugaba Jonathan, Reno Omokri, ya wallafa a ranar 24, ga Afrilu, 2021 wata biyu kafin zaben 2015 ya nuna kalaman Fashola na cewa:

“Samar da wutar lantarki ba abin da zai gagara ba ne. Kamar janareto ne —kamar hada kananan injinan janareto guda miliyan daya ne a wuri daya.

“Idan aka samar da guda daya kai karfin kilowatt daya, za a iya yin babba wanda zai samar da megawatt 1,000…

“Amma duk da biliyoyin dalolin da ake ta kashewa, har yanzu muna cikin duhu, kullum sai karya gwamnati take yi mana, amma samar da wutar lantarki ba abun da ba zai yiwu ba ne.

“Ina fada da babbar murya cewa rashin kwarewar shugabanninmu ne ya sa muke fama da rashin wutar, amma ba wai ba za a iya samar da ita ba.

“Shi ya sa abokan aikina ke kiran su da ’yan koyo,” inji Fashola a taron zagayowar ranar haihuwar Bola Tinubu, karo na bakwai.

Bayan cin zaben 2015, Buhari ya nada shi Minitan Wutar Lantarki, Ayyuka da Gidaje, nan take ya kaddamar da muradunsa na ‘Samar da Kari da Tabbaciyar Wutar Lantarki’.

Mako hudu bayan nan ne (8 ga Disamba, 2015) ya yi taron ’yan jarida inda ya koka kan karancin kudaden kasafin ma’aikatun, bayan an hade su a wuri daya.

Ya kuma kaddamar da shirin karfafar Hukumar Samar da Lantarki ta Kasa (TCN) da kuma tabbatar da cewa kamfanonin taruwa (Gencos) da samar da wutar (Gencos) sun kara zuba jari a bangaren.

A watan Fabrairun 2016 aka yi karin wutar kudin lantar, wanda ya zama amsa babban kalubale, a matsayinsa na mai kula da Hukumar Kula da Farashin Wutar Lantarki, (NERC).

A tsawon wa’adinsa, NERC ta shekara guda ba tare da kwamitin daraktoci ba, ita kuma TCN har ya sauka ba a nada kwamitin daraktoci ba.

Ayyukan Fasola na wutar lantarki

Sau bakwai a lokacinsa, NERC na kasa sabunta farashin lantarki, wanda hakan ya haddasa asarar kimanin Naira tiriliyan daya —bayan karin da ka ayi a 2016 ya fusata ’yan Najeriya.

Fashola ya fara aiki a lokacin da karfin wutar lantarki da ake samarwa ya hauwa megawatt 5,500, amma zuwa lokacin da aka sauke shi, karfin ya ragu zuwa megawatt 3,375.

Uwa uba, an ci gaba da samun tangal-tangal, dauke wuta da lalacewar tashoshin wutar lantarki a lokacin nasa.

Sai dai wutar da ake turawa ta karu da megawatt 6,000 zuwa 7,000, yayin da karfin wutar da ake samarwa ya karu daga 5,500MW a shekarar 2015 zuwa 8,100 a 2018.

Kazalika, karfin wutar da ake rabawa ta karu daga 4,500MW a shekarar 2015 zuwa 5,375 a shekarar 2019.

Me Sale Mamman ya yi?

Mun nemi sanin abin da zuwa yanzu minista mai ci, Sale Mamman ya yi, amma hadiminsa, Hakeem Bello, ya ce sai dai mu ba shi a rubuce.

“Idan kuna so ku yi irin wannan labarin sai ku rubuto mana saboda mu san abin da labarin zai mayar da hankali a kai, saboda ban fahimci yadda kuke kokarin hada wadannan abubuwa marasa alaka ba,” inji shi.