✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bayan cizon jar hula, Ganduje ya ga samu ya ga rashi cikin awa 24

Sai dai duk da cizon jar hular da Ganduje ya yi, matashin ya koma Kwankwasiyya

A wani yanayi mai kama da ta leko ta koma, ana iya cewa Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya ga samu ya ga rashi bayan da matashin da aka gan su tare a hoto ya sauya sheka daga NNPP zuwa APC, ya yi mi’ara koma baya.

A ranar Laraba ce dai wani matashin dan siyasa kuma dan gaba-gaba a tafiyar Kwankwasiyya a Jihar, Yusuf Sharada, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar NNPP.

Matashin ya dauki matakin ne bayan jam’iyyar ta fitar da jerin sunayen ’yan takararta na masalaha, amma ya ga babu sunan shi, kan bukatar shi ta neman takarar kujerar Majalisar Tarayya daga mazabar Birnin Kano da Kewaye.

Hakan ce ta sa ya sanar da ficewa daga jam’iyyar tare da komawa APC, inda har Gwamna Ganduje cizon jar hular Sharadan bayan ya cire ta daga kan shi.

Lamarin dai ya yi ta tada kura a Jihar, musamman a shafukan sada zumunta na zamani.

A cewar wani mai goyon bayan Ganduje, kuma Shugaban Karamar Hukumar Nassarawa da ke Jihar ta Kano, Lawan Shuiabu Aranposu, “Lamarin dai ya yi ta tada kura a Jihar, musamman a shafukan sada zumunta na zamani.”

Ganduje tare da Yusuf Sharada bayan cire masa jar hula
Ganduje tare da Yusuf Sharada bayan cire masa jar hula

Shi kuwa Adnan Mukhtar Tudun Wada, mai neman takarar kujerar Majalisar Jiha daga mazabar Nassarawa  PDP, cewa ya yi, “Yanzu zaka samu yanci a siyasance, zaka samu walwala. Dama ita siyasa a haka take. Na sanka a matsayin haziki kuma jajirtacce a wancan tsarin. Abinda kayi shine sanin mutuncin kai kuma ka tabbatar da cewa kana da raayin gaske.

“Kayi hakuri da duk abinda za ace, za a zageka, za aci mutuncinka, a kira ka da maci amana da butulci amma tabbas ni na tabbatar da nagartarka.

“Allah ya tabbatar maka da alkairin sa Yusuf Sharada,” inji Adnan.

To sai dai cikin kasa da awa 24, Yusuf Sharada ya yi amai ya lashe, inda ya sanar da sake komawar shi NNPP, bayan ya ce ya yi shawara da iyaye da makusantan shi.

Sharada ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Alhamis cewa, “Ni Yusuf Sharada Ina sanar da mutane cewa gaskiya ne jiya mun gana da gwamna Ganduje, bayan komawar Jagora Rabiu Kwankwaso Abuja. Ajizanci na Dan Adam ya jani ga yanke hukunci wanda bai yiwa ‘yan uwa da masoya dadi ba. Ina bawa dukkan wanda wannan abu da nayi ya batawa rai hakuri.

“Matsayar dana dauka ta samu rashin goyon bayan iyaye, ‘yan uwa da abokan arziki daga sassa daban daban na kasar nan.

“Gwamna Ganduje bai bani koda naira daya ba, kuma offer daya bani nayin aiki dashi na hakura da ita.

“Zan cigaba da yin abinda aka sanni akansa, in shaa Allah. Kwankwasiyya Amana!,” kamar yadda ya wallafa.

Sai dai su ma magoya bayan Kwankwasiyya sun shiga tofa albarkacin bakunansu kan lamarin.

“Yanzu cizon da Baba Dan Audu ya yiwa Hular Ulama Yusuf Sharada ya tashi a Banza?” inji wani dan Kwankwasiyya mai suna Aminu Sulaiman Janbirji.

Shi kuwa Amb Zahraddeen Idris Sulaiman cewa ya yi, “Ulama Yusuf Sharada Ka Kyauta Da Ka Dawo. Amma Ina Baka Shawara Ka Koma Ka Karbo Jar Tagiyar Ka Ta Wajen Moddibo Kafin Ya Hadiyeta”.

A ranar Larabar ce dai NNPP wacce tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ke yi wa jagoranci, ta fitar da sunayen ’yan takararta na masalaha a Jihar Kano a dukkan makamai, inda wasu suke ganin ba a yi musu adalci ba a ciki.

Sharada dai yana cikin wadanda suka ci gajiyar tallafin karatu a zamanin mulkin tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.