✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bayan fitowa da gidan yari, Dariye zai yi takarar Sanata

Ranar Litinin aka sako Sanata Dariye daga Gidan Yarin Kuje bayan shekara hudu a daure

Tsohon Gwamnan Jihar Filato, Joshua Dariye, wanda aka sako daga gidan yari ranar Litinin zai tsaya takarar Sanatan Filato ta Tsakiya.

Dariye wanda aka yi wa afuwa bayan ya shekara hudu da cikin shekara 10 da aka yanke masa a kurkurku kan badakalar Naira biliyan 1.26, zai yi takara ne a Jam’iyyarsa ta LP.

Wani jami’in Jam’iyyar LP da ya nemi a boye sunansa ya ce: “Gaskiya ne, [Dariye] zai yi takarar sanata; Muna shirye-shiryen zuwansa Abuja domin bayyana aniyarsa.”

A cewarsa, tsohon gwamnan zai ba da mamaki a zaben, sbaoda har yanzu mutanen Jihar Filato suna kaunar sa.

Ya kuma ce dawowar tsohon gwamnan zai kara wa dan takarar LP na gwamnan jihar, Patrick Dakum, damar lashe zabe saboda gazawar Jam’iyyar APC mai mulkin jihar.

Wata majiya mai karfi ta shaida wa Aminiya cewa Hedikwatar Jam’iyyar LP da ke Abuja ya kammala shirye-shirye domin zuwa Mista Dariye sayen fom din takara.

Bayan Dariye ya mulki Jihar Filato a karkashin Jam’iyyar PDP ne ya sauya sheka zuwa Jam’iyyar LP, inda ya lashe zaben Sanata a zaben 2011.

Aminiya ta yi kokarin samun karin bayani daga Shugaban Jam’iyyar LP Reshen Jihar Filato, amma hakarta ba ta cimma ruwa ba.

Ranar Litinin aka saki Dariye da tsohon Gwamnan Taraba, Jolly Nyame, daga Gidan Yarin Kuje, wata shida bayan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi musu afuwa.

A ranar 14 ga watan Fabrairu ne tsoffin gwamnonin da wasu mutum uku suka samu afuwar Shugaban Kasa bayan zaman Majalisar Shugabanni ta Kasa.