✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Bayan guduwar miji da watanni takwas, kotu ta kashe aurensa a Kano

Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke zaune a unguwar Dorayi cikin birnin Kano, ta raba auren wasu ma’aurata da suka shafe shekaru shida da aure…

Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke zaune a unguwar Dorayi cikin birnin Kano, ta raba auren wasu ma’aurata da suka shafe shekaru shida da aure kan kaurace wa matar da mijin ya yi na tsawon watanni takwas.  

Matar wadda ta kasance uwar ‘ya’ya biyu da ta samu a auren nasu, ta shaida wa kotun cewa, maigidan nata ya gudu ya barta da yaran na tsawon watanni takwasba tare da waiwayarsu ba.

Ta ce, “Ya Mai shari’a tun wancan lokacin bani da lafiya kuma na dauki tsawon lokaci ina shan bakar wahala.

“Bana iya biya wa yarana kudin Makaranta kuma basu samun wadataccen abincin da za su ci su koshi saboda mijin ya tsere ya kyaleta da dawainiya, in ji ta.

A na shi bangaren, Kawun mijin nata mai suna Malam Ibrahim ya bayyana wa Kotun cewa, shi kansa bashi da masaniyar inda mijin nata ya shiga.

A karshe dai Alkalin Kotun, Mai Shari’a Malam Umar Dan-Baba, ya yanke hukuncin katse igiyar auren, domin a cewarsa hakan shi ne mafi a’ala.