✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Bayan kwana 11 a tsare, ’yan bindiga sun sako daliban Zamfara

Hakan na zuwa ne bayan gwamnati ta katse hanyoyin sadarwa a Jihar.

Daliban da ’yan bindiga suka sace daga Makarantar Sakandiren Gwamnati da ke garin Kaya a Karamar Hukumar Maradun ta Jihar Zamfara sun shaki iskar ’yanci.

Gidan Talabijin na Najeriya (NTA) ne rawaito labarin, inda ya ce, “Daliban Makarantar Sakandiren Gwamnati da ke Kaya a Karamar Hukumar Maradun ta Jihar Zamfara sun kubuta daga hannun ’yan bindiga bayan sati biyu a tsare.”

Hakan na zuwa ne bayan gwamnati ta katse hanyoyin sadarwa a Jihar a yunkurin da take yin a kawo karshen ayyukan ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane a Jihar.

Wani sashe na daliban GDSS Kaya a Jihar Zamfara da suka kubuta  Hoto: NTA
Wani sashe na daliban GDSS Kaya a Jihar Zamfara da suka kubuta
Hoto: NTA

Har yanzu dai babu cikakkun bayanai akan kubutar daliban, in banda wasu hotunansu guda biyu da gidan talabijin din ya wallafa a shafinsa na Facebook.

’Yan bindigar dai sun kutsa kai makarantar ce wacce take mahaifar Gwamnan Jihar, Bello Matawalle, sannan suka sace dalibai da wani malaminsu.

Sai dai daga bisani biyar daga cikinsu sun tsere daga hannun masu garkuwar.

Masana harkokin tsaro dai na cewa da alama kwalliya na biyan kudin sabulu a matakan da gwamnati ke ci gaba da dauka a yanzu haka a Jihar la’akari da yadda wadanda aka yi garkuwa da su suke ta kubuta.

Lamarin dai ya jefa ’yan bindigar cikin tsaka mai wuya sakamakon ba sa samun hanyoyin sadarwa da junansu ko masu basu bayanai ko kuma samun damar shiga kasuwanni don yin sayayya.

A makon da ya gabata, Gwamna Matawalle ya ce luguden da ake ci gaba da yi wa ’yan bindigar ya sa wasu daga cikinsu sun fara neman a yi sulhu, amma ya ce gwamnatinsa ba zata sake yin sulhu da su ba.

A madadin haka, ya ce za a ci gaba da zafafa kai musu hare-hare har sai an ga bayansu.