Bayan mako 2 ’yan bindiga sun sako Uwar Marayu | Aminiya

Bayan mako 2 ’yan bindiga sun sako Uwar Marayu

    Ahmed Ali, Kafanchan

An sako malamar Kwalejin Kimiyya da Kere-Kere ta Kaduna, Injiniya Rahmatu Abarshi, wadda a Uwar Marayu, bayan shafe fiye da mako biyu a hannun ’yan bindiga.

A cikin watan Ramadan da ya gabata ne aka yi garkuwa da Doka Abarshi ne tare da ’yarta Ameerah da direbanta, ranar 24 ga Watan Afrilu a kan hanyar Kachia zuwa Kaduna yayin da suke dawowa daga rabon kayan tallafi ga marayu a kauyen Mariri da ke Karamar Hukumar Lere ta Jihar Kaduna.

Daya daga cikin ma’aikatanta, wanda kuma ya tsallake fadawa hannun ’yan bindiga a ranar, Abdallah Isma’il Abdallah, ya shaida wa da Aminiya cewa an sako malamar a ce ranar Talata, amma ’yan bindigar sun ci gaba da rike ’yarta da kuma direbanta.

“Ita kadai kawai suka sako kuma a halin yanzu ba ta iya magana saboda kidimewa, a yanzu haka an wuce da ita asibiti don duba lafiyarta,” inji shi yayin da yake bayyana wa Aminiya halin da ake ciki.