✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bayan nasara 15 a jere, shin an karya lagon Xavi da Barcelona ne?

Wannan na nuna da alama Barcelona za ta karkare kakar bana ba tare da kofi ba

Bayan doke Barcelona da kungiyar Eintracht Frankfurt ta Jamus ta yi da ci uku da biyu a gidan Barcelona, wanda hakan ta kawo karshen jerin wasannin da kungiyar ta yi a karkashin sabon kocinta Xavi ba tare da an doke ta ba.

Wannan karya lagon Xavin da aka yi ya nuna da alama Barcelona za ta karkare kakar bana ba tare da kofi ba.

An cire kungiyar a gasar Europa da Copa del Rey, sannan ita ce ta biyu a Gasar Laliga, inda Real Madrid ta ba ta tazarar maki 12 da kwantan wasa daya, sannan saura wasa takwas a karkare kakar.

Tun bayan zuwan Xavi kungiyar aka samu sauyin sakamakon wasanni, wanda hakan ya sa ko a makon jiya tsohon dan wasan kungiyar, Ronaldinho ya ce ya ga alamar kungiyar za ta lashe kofuna a bana.

Xavi ya karbi ragamar horar da Barcelona ne a watan Nuwamban bara, inda tun lokacin zuwa yanzu ya jagoranci kungiyar a wasa 27.

A cikin wasannin, ya samu nasara a wasa 27, canjaras 15 sannan aka doke shi say biyar.

Babban abin da ya fi daukar hankalin jama’a shi ne yadda kungiyar ta kwashe wasannin guda 15 a jere ba tare da ta yi rashin nasara ba a karkashin sabon kocin.

To sai dai kuma Barcelona ta yi wasa 14 a jere a dukkan fafatawa ba tare da yin rashin nasara ba, karkashin Xavi.

Rabon da aka doke kungiyar a karkashin Xavi, tun wasanta da Real Madrid a 12 ga watan Janairun 2022 da Real Madrid din ta doke ta da uku da biyu gasar a Spanish Super Cup a Saudi Arabia.

Wannan ya sa ake zaton Barcelona din ce za ta lashe Gasar Europa na bana, ganin irin tashen da take yi, kafin Frankfurt ta mata shigo-ba-zurfi.

Me ya faru?

A daidai lokacin da Barcelona ke kokarin kare martabarsu, sai dan wasan Frankfurt, Filip Kostic ya zura kwallo a ragar Barcelona a minti hudu da fara wasa.

Ana cikin haka ne Rafael Borre ya zura na biyu.

Ana cikin haka ne sai Kostic ya zura na uku a minti 67 da fara wasa, wanda hakan ya sa hankali ya tashi. Magoya bayan Barcelona ciki ya duri ruwa, ‘yan adawansu kuma suka fara tururuwan zuwa kallo da murna.

Barcelona ta farke kwallo biyu daga bisani, amma ba su samu farke na ukun ba.

Bayan wasan, kocin Barcelona Xavi ya ce lallai Frankfurt ta cancanci lashe wasan, sai dai ya ce yawan magoya bayan kungiyar Frankfurt da suka zo bakunci a Camp Nou ya taimaka wajen karya musu gwiwa.

Shi ma Shugaban Kungiyar Barcelona ya ce a bincika masa yadda aka yi magoya bayan kungiyar Frankfurt din suka taru a filin wasan, bayan an samu magoya bayan kungiyar su 30,000 a filin.

A wani bangaren kuma, wasu magoya bayan Barcelona suna ganin rashin farawa da dan wasa De Jong ya taimaka wajen ba Frankfurt damar mallakar tsakiyan filin, wanda kuma shigowarsa daga baya an ga canji.

Haka kuma bayan rashin De Jong din, shi ma kyaftin din Barcelona Bosquet ya tsufa, inda yanzu ba ya iya kazar-kazar kamar da.

Akwai kuma batun tashe da Barcelona ke yi, wanda ya ‘yaudari’ ‘yan wasan Barcelona suke ganin za su lallasa Frankfurt din a gidansu.

Shi ke nan an karya lagon Barcelona?

Ganin an cire Barcelona, kuma da wahala su ci wani kofi a kakar bana, sai wasu suke tunanin ko an karya lagon Barcelona da Xavin ke nan.

Sai dai binciken Bakin Raga ya gano Barcelona ba ta da wasu wasanni masu zafi a gaba.

Haka kuma kasancewar har yanzu Xavi gyara yake yi, da kuma ganin zai yi wahala ya wuce na biyu, zai fi mayar da hankalinsa kakar badi.

Haka kuma matsalar tattalin aziki da kungiyar ta shiga yanzu an samu sauki, ke nan badi za su saya ‘yan wasa sabbi.