✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bayan shafe mako 4 a tsare, ’yan bindiga sun sako daliban Kwalejin Zariya

Mutanen dai sun shafe kusan makonni hudu a tsare.

Bayan shafe kusan mako hudu a tsare tun bayan sace su, ’yan bindiga sun sako daliban Kwalejin Fasaha ta Nuhu Bamalli da ke Zariya a Jihar Kaduna.

Zuwa lokacin kammala wannan rahoto, daliban suna kan hanyar na komowa daga inda aka dauko su domin su koma ga iyalansu.

Idan ba a manta ba, a ranar Alhamis, 10 ga watan Yunin da ya gabata ne ’yan bindiga suka kutsa kai cikin makarantar suka kashe dalibi daya, suka raunata wani sannan suka yi awon gaba da dalibai da malamai mutum 10.

Dalibin da ya rasu mai suna Ahmad Abdulhameed dai na karantun Babban Difiloma ne a fannin Kididiga sai wanda aka harbe shi a cinyarsa mai suna Haruna Isiyaku Duna, wanda shi ma yake karatu a karatun a sashen.

Daga cikin malaman da ’yan bindigar suka tafi da su a kwai Mista Habila Nida’i da Malam Adamu Shehu Shika da ke fannin karatun Tsimi da Tanadi.

Sai dai daga bisani ’yan bindigar sun sako matar Malam Ahmad Abdul da ’ya’yanshi kanana biyu saboda ta kasa tafiya saboda tsohon cikin da take dauke da shi.

Sai dai wata majiya ta ce sai da aka biya kudin fansa kafin a sako su.

Ko da yake mai maganana da yawun hukumar makarantar, Abdullahi Ibrahim Shehu ya ce su dai a hukumance ba su ba da ko sisi ba kuma bai san ko an ba da wani abu ba kafin a sako su.