✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bayan shan kaye a kotu, Ganduje ya lallashi magoya bayansa

Ganduje ya ce tunda rikicin cikin gida ne jam'iyyar da gwamnatin jihar za su lalubo mafita

Gwamnan Jihar Kano, Abduullahi Ganduje, ya yi kira ga magoya bangarensa na jam’iyyar APC a jihar da su kwantar da hankalinsu duk da kayen da bangaren ya sha a kotutun daukaka kara.

Ganduje ya yi kiran ne bayan Kotun Daukaka Kara da ke zamanta a Abuja ta soke zaben shugabannin jam’iyyar a matakin jiha da bangarensa ya gudanar.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Hamza Mu’azu ya kuma tabbatar da shugabannin da bangaren da tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, yake jagoranta, ya zaba a matsayin halastattu.

Ya kuma ci bangaren Ganduje tarar Naira miliyan daya tare da umartar uwar jam’iyyar ta kasa ta yi mu’amala da Alhaji Ahmadu Haruna Zago da sauran shugabannin bangaren Shekarau a matsayin halastattun shugabannin APC na jihar Kano.

Sanarwar da Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Kano, Muhammad Garba, ya fitar ta ce tunda rikici ne na cikin gida a jam’iyyar, gwamnatin jihar da jam’iyyar na nazari kan lamarin domin lalubo mafita.

“Ganduje ya umarci jami’an tsaro da kar su raga wa duk wani mai karya doka, domin gwamnati ba za ta lamunci duk wani nau’i na karya doka ba da sunan siyasa.”

Ya kuma bayyana godiyarsa ga ’yan jam’iyyar bisa goyon baya da kwarin gwiwar da suke ci gaba da bayarwa.