✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Bayan shan kaye, Sanata ya sa deliget su dawo da motocin da ya ba su

Sanata Akinyelure ya bai wa daliget wa'adin 24 su dawo da motoci da dalolin da ya ba su, tunda ya rasa tikitin neman komawa kan…

Dan takarar Sanata karkashin Jam’iyyar PDP a Jihar Ondo, Ayo Akinyelure, ya kwace motocin da ya bai wa daliget a mazabarsa bayan da ya sha kaye a zaben tsayar da dan takarar jam’iyyar.

Sanata Akinyelure mai son ci gaba da zama a Majalisar Dattawa, ya sha kaye ne a hannun abokin takararsa, Ifedayo Adedipe, a zaben fid da gwanin da jam’iyyarsa ta PDP ta gudanar.

Yayin zaben, Ifedayo Adedipe ya tashi ne da kuri’a 82 yayin da Sanata Akinyelure ma ci ya samu kuri’u 58.

Cif Segun Adegoke na daga cikin daliget din da lamarin ya shafa, inda Akinyelure ya ba shi wa’adin sa’a 24 ya dawo mishi da dalolin da ya ba shi kafin zabe.

Da yake kare muradin uban gidansa, mai magana da yawun Sanatan, Charles Akinwon, ya ce daliget din sun saba yarjejeniyar da suka cin ma wa da maigidan nasa, shi kuma maigidan nasa ya bukaci su dawo masa da dukiyar da ya ba su.

Ya kara da cewa, daliget din da lamarin ya shafa sun gaza wajen cika alkawarin da suka daukar wa maigidansa na za su kada masa kuri’un da za su ba shi damar cin zaben dan takarar.