✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bayan shekara 100 Sarautar Zazzau ta koma gidan Mallawa

Masu zabar Sarki na Masarautar Zazzau sun yi mubaya'a ga Sarki na 19, Ahmed Nuhu Bamalli

Sabon Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli ya isa fadarsa da ke Zariya, bayan gwamnatin Jihar Kaduna ta sanar da nadinsa.

Ahmed Bamalli shi ne Sarkin Zazzau na farko daga gidan Mallawa, tun bayan rasuwar kakansa, Sarki Dan Sidi shekaru 100 da suka wuce (1920).

Ya zama Sarkin Zazzun ne kwana 17 bayan rasuwar Sarki na 18, Alhaji Shehu Idris wanda ya rasu ranar 20 ga Satumba, 2020 bayan shafe shekara 45 kan mulki.

Sarki Shehu Idris wanda ya rasu yana da shekara 85 a duniya sakamakon rashin lafiya shi ya fito ne daga gidan sarauta na Katsinawa.

Masarautar Zazzau na da gidajen sarauta hudu da suka hada da gidan Katsinawa, Mallawa, Barebare da kuma gidan Fulani.

Kafin nadin shi, Sariki Bamalli shi ne Magajin garin Zazzau, mukamin da ya gada bayan rasuwar mahaifinsa Alhaji Nuhu Bamalli.

Sarkin wanda aka haifa a 1966, shi ne tsohon Jakadan Najeriya a kasa Thailand, kuma tsohon Manajan-Darakta a kamfanin buga takardun kudi na Najeriya.

Tsohon Kwamishina na Kasa ne a Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) sannan ya yi aiki a matsayin Babban Jami’in Hulda da Jama’a a kamfanin sadarwa na Mtel —reshen tsohon Kamfanin Sadarwa na Najeriya (NITEL).

Ya yi karatunsa na digirin farko a Jami’ar Ahamdu Bello (ABU) da ke Zariya, bayan halartar makarantun firamare da sakandare a Kaduna.

Ya samu digiri na biyu a Jami’ar Oxford a fannin Mu’amalar Kasa da kasa da kuma Shugabancin Kamfanoni.