✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bayan shekara 11 AC Milan ta sake lashe gasar Serie A

Karo na 19 ke nan jimilla da Milan ta lashe babbar gasar Italiya ta Serie A a tarihi.

Bayan shekaru 11 kungiyar kwallon kafa ta AC Milan ta lashe gasar Serie A ta bana da maki 86.

Nasarar Milan na zuwa ne bayan ta doke Sassuolo da ci 3-0 a wasan ranar karshe na gasar da aka fafata a Yammacin ranar Lahadi.

Milan dai na bukatar cinye wasanta da Sassuolo kafin ta iya daga kofin, yayin da babbar abokiyar hamayyarta, Inter Milan ta kare a mataki na biyu da tazarar maki biyu tsakaninsu.

’Yan wasan na Stafano Pioli sun jinjina kofin duk da nasarar da Inter ta yi 3-0 kan Sampdoria.

Olivier Giroud ne ya zira kwallo biyu a wasan kafin daga baya Frank Kessie ya ci ta uku duk a cikin minti 36 kacal da soma wasan.

Karo na 19 ke nan jimilla da Milan wadda ake yi wa lakabi da Rossoneri ta lashe babbar gasar Italiya ta Serie A a tarihi.