✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bayan shekara 20 da konewa, gwamnati za ta sake gina babbar kasuwar Jos

Kasuwar dai ta kone ne tun shekarar 2002

Majalisar Zartarwar Jihar Filato ta amince da fara aikin sake gina babbar kasuwar birnin Jos da ta kone kimanin shekara 20 da suka wuce.

Majalisar ta amince da fara aikin sake gina wannan kasuwa ne yayin taron da ta gudanar a garin Jos.

Da yake yi wa manema labarai karin bayani, bayan kammala taron majalisar, Kwamishinan yada labarai na Jihar, Mista Dan Manjang, ya ce aikin na daya daga cikin ayyukan raya kasa da Gwamnan Jihar, Simon Lalong, ya bai wa muhimmanci.

Sai dai ya ce akwai yiwuwar a dauki dogon lokaci ba a fara aikin ba, saboda tsauraran sharddan da ’yan kasuwa masu zuba jari da ke son yin aikin suke gindayawa.

Ya ce an kulla yarjejeniya tsakanin gwamnatin Jihar da Bankin Jaiz wanda shi ne zai bayar da bashin dukkan kudaden da za a yi amfani da su wajen wannan aikin.

Sai dai ya ce suna sa ran za a kammala aikin kafin karshen wa’adin wannan gwamnatin.

Da yake bayani kan yarjejeniyar aikin, Kwamishinan Raya Birane na Jihar, kuma wanda yake rikon Ma’aikatar Ciniki da Masana’antu ta Jihar, Alhaji Idris Gambo, ya ce za a gina shaguna manya da kanana guda 4,231 wanda zai dauki kashi 44 na filin kasuwar.

Ya ce ragowar filin kasuwar kuma za gina wajen tsayawar motoci da bankuna da ofishin jami’an kashe gobara da ’yan sanda da kuma na hukumar gudanarwar kasuwar.

Kwamishinan ya ce kasuwar mallakin gwamnatin Jihar ce, don haka hukumar gudanarwar kasuwar ce, za ta cigaba da gudanar da ita, a yayin da wadanda suka zuba kudadensu za su fitar da su wajen sayar da shagunan kasuwar.

Ita dai wannan kasuwa wadda ta kone tun a shekara ta 2002, an kiyasta za a kashe Naira biliyan tara da Naira miliyan 400, a yayin aiki na sake gina ta.