✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Bayan shekara 30, Kwalejin Ilimi ta yi bikin yaye dalibai a Gombe

Rabon kwalejin da irin wannan bikin tun shekarar 1991/1992.

Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Gombe ta gudanar da bikin yaye dalibanta, bayan shafe shekara 30 ba tare da yin hakan ba.

Tun shekarar 1991/1992 kwalejin ta gudanar da bikin kuma ba ta sake yin haka ba sai a wannan karon.

Da yake jawabi a wajen bikin, Shugaban kwalejin, Dokta Ali Adamu Boderi, ya ce a cikin shekara 30 din, makarantar ta yaye dalibai masu takardar shaidar karatu na NCE guda 20,000, yanzu kuma ta fara koyar da Digiri da hadin guiwar Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi (ATBU) da kuma Jami’ar Maiduguri.

Dokta Boderi, ya kuma ce a lokacin bikin, kwalejin ta ba da lambar karramawa wa Gwamnan Jihar, Muhammad Inuwa Yahaya da Ministan Sadarwa, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, da kuma mai martaba Sarkin Gombe, Alhaji Abubakar Shehu Abubakar III

Sannan ya hori daliban da aka yaye da su yi amfani da abin da suka koya na ilimi da na sana’a don ya amfanesu a rayuwarsu.

Shi ma a nasa jawabi Ministan Ilimi Malam Adamu Adamu, ya ce yanzu haka Gwamnatin Tarayya ta saki kudi Naira biliyan shida don inganta tsarin koyarwa a wasu kwalejojin iliminta guda shida a fadin Najeriya.

Ministan wanda ya samu wakilcin Babban Sakataren Hukumar Kula da Kwalejojin Ilimi (NCCE), Farfesa Paulinius Okwelle, ya ce kudaden an bayar da su ne ta wajen shirin TETFund.

Daga nan ya ce kowacce kwaleji za ta karbi Naira biliyan daya domin fara gudanar da ayyukan.