✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bayan shekara 41 yana jan Tarawihi, Limamin masallacin Madina ya yi murabus

Ana dai tunanin hakan ba zai rasa nasaba da shekarunsa ba

Bayan shafe tsawon shekara 41 yana jagorantar sallolin Tarawihi da Tahajjud, Sheikh Ali Ibn Abdurrahman Alhudaifi, ba ya cikin limaman da za su jagoranci Sallah a masallacin Annabi (S.A.W) a Azumin bana.

Shafin masallatan Harami da ke kasar Saudiyya na Haramain Sharifain ne ya sanar da haka, a cikin wani takaitaccen sako da ya wallafa a Facebook ranar Lahadi.

Sai dai sanarwar ba ta yi cikakken bayani kan dalilin da ya sa bana ba ya cikin wadanda za su jagoranci sallar ba kamar a baya, kodayake ana ganin hakan ba zai rasa nasaba da shekarunsa ba.

A cewar shafin, “Bayan tsawon shekaru, Sheikh Ali Al Hudaify ba zai jagoranci sallolin Tarawihi da Tahajjud a Masallacin Annabi [S.A.W] da ke birnin Madina a bana.”

Binciken Aminiya ya gano cewa Sheikh Alhudaifi ya fara limancin sallolin ne tun a shekarar 1981 a masallacin.

Mai kimanin shekara 75 a duniya, limamin ya yi suna ne da irin zakin muryarsa wajen rera karatun Alkur’ani yayin gudanar da sallolin.

Ko a shekarar 2016 dai sai da hukumomin kasar ta Saudiyya suka cire babban mai ba da fatawa, Abdul Aziz Abdullahi Ali Sheikh daga cikin masu huduba a dandalin Arafat lokacin Aikin Hajji, bayan ya shafe shekara 35, shi ma saboda tsufa.