✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bayan shekara 7, Zulum ya sabunta Makarantar Chibok

An sauya wa makarantar suna da kuma tsari bayan sabuntawar.

Gwamnan Borno, Babagana Zulumn ya sabutan Makarantar Sakandaren ’Yan Mata (GGSS) da ke garin Chibok, inda kungiyar Boko Haram ta sace dalibai 276 a makarantar a shekarar 2014.

Sace daliban da kungiyar ta yi shekara bakwai da suka gabata ta sa wasu dubban dalibai kaurace wa zuwa makarantu a Jihar na tsawon lokaci.

Da yake jawabi, a wurin bude da makarantar, Zulumn ya ce, “Makarantar na da ajujuwa da dakin karatu da dakin gwaje-gwaje da cibiyar sadarwar zamani (ICT) da asibiti da kuma filin wasu, duk na zamani.

“Sannan, domin tabbatar da tsaro, akwai dakin jami’an tsaro da babbar kofar shiga makarantar, akwai kuma wuraren yin sintiri, kowannensu da jami’an tsaro masu wadatattun kayan aiki.”

Ministar Harkokin Mata, Pauline Tallen, ce ta kaddamar da makarantar da aka sauya wa suna zuwa Makarantar Sakandaren Gwamnati (GSS) Chibok aka kuma mayar ta samari da ’yan mata.

Ta yaba wa Gwamnatin Zulum kan aikin sabunta makarantar, tana mai cewa gwamnati ta tashi haikan wajen yakar ta’addanci da kuma inganta bangaren ilimi musamman na ’ya’ya mata.

“Ina rokon shugabannin Chibok da su ci gaba da bayar da cikakken goyon bayansu ga gwamnatin Gwamna Babagana Zulum wanda a koyaushe a shirye yake domin yi wa ilimin ’ya’ya mata gata,” inji ta.

Tun bayan harin Boko Haram a shekarar 2015, Gwamnatin Tarayya ta Goodluck Jonathan ta yi alkawarin gyara ta, amma daga baya Gwamantin Jihar Borno ta karbe aikin ta kuma aiwatar da shi.

A tsawon shekara bakwai da Boko Haram ta sace daliban, an yi kubutar da da dama daga cikinsu, amma rahotanni sun ce an aurar da 112 daga cikin su ga mayakan kungiyar har sun haihu da su.

“Muna jajanta wa al’ummar Chibok saboda mun san halin da kuke ciki, amma nin tabbatar muku cewa muna aiki ka’in da na’in domin ganin ku da sauran yakunan da ayyukan ta’addanci suka shafa kun koma gudanar da rayuwarku yadda kuka saba a baya,” inji ministar.

Zuluma ya ce, “Gwamnatinmu ta yi alakwarin sabunta GGSS Chibok da ’yan ta’adda suka lalata, kuma ina farin cikin ganin kaddamar da aikin da aka kammala.

“Muna so mu ga dalibai sun koma makaranta su samu ilimin da suke bukata domin yin rayuwa mai inganci; za ba karfafe su da duk abin da ya dace, mu kuma taimaka wa iyayensu da al’ummar baki daya.

“Sannan ba mu manta da ’Yan Matan Chibok ba, muna aiki kai da fata gomin ganin sun dawo wurin iyayensu.”

Da take jawabi, Shugabar Makarantar, Asabe Ali Kwongla, ta bukaci gwamnati da ta saki samar da kaya a dakin gwaje-gwajen, karin malami da kuma babura masu kafa uku, saboda ko da wani abu na gaggawa zai iya tasowa.