✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bayan shekaru 15 Bafarawa ya kai ziyara gidan Wamakko

Tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa ya ziyarci Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko har gida a karon farko bayan tsawon shekaru 15. Bafarawa ya…

Tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa ya ziyarci Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko har gida a karon farko bayan tsawon shekaru 15.

Bafarawa ya ziyarci gidan ne domin yi wa Sanata Wamakko ta’aziyar rasuwar dan uwansa, Dokta Bello Magatakarda Wamakko wanda ya rasu ranar Asabar bayan ya yi fama da ‘yar gajeruwar rashin lafiya.

Bafarawa tare da tawagarsa wacce ta kunshi abokanansa na siyasa da ‘yan uwansa da kuma hadimai, sun yi gaisuwa ga dangin marigayin wanda ajali ya katse masa hanzari a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.

An gudanar da addu’o’i na musamman wanda babban limamin masallacin Juma’a na Usman bin Affan, Shaikh Yahuza Shehu Tambuwal ya gabatar.

Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya dawo gidansa da ke unguwar Gawon Nama a shekarar 2006, bayan da alaka ta yi tsami tsakaninsa da Bafarawa wadda ta kai da har ya ajiye aiki a matsayin mataimakin gwamna jihar Sakkwato.

Tun daga wancan lokaci gabanin yanzu, Bafarawa bai taba taka kafarsa a gidan ba domin taya murna ko jaje, sai a wannan karo da suka sulhunta rashin ‘yar ga macijin da ke tsakaninsu.