✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Bayan umarnin Buhari, sojoji na samun nasara kan ’yan ta’adda

Ministan Yada Labarai da Raya Al’adu, Lai muhammad, ya ce umarnin da Shugaban Kasa  Muhammadu Buhari ya bawa sojoji na farautowa, da yi wa ’yan…

Ministan Yada Labarai da Raya Al’adu, Lai muhammad, ya ce umarnin da Shugaban Kasa  Muhammadu Buhari ya bawa sojoji na farautowa, da yi wa ’yan ta’dda magana da yaren da suke fahimta ya san an fara samun galaba a kansu.

Ministan ya bayyana hakan ne ranar Talata, yayin wani taron kasa kan rawar da ’yan jarida za su taka wajen raya al’ada, da zaman lafiya a Najeriya, wanda cibiyar wayar da kai kan muhimmacin al’adu (NICO) ta shirya a Kano.

“Dakarunmu sun sanar da mu irin nasarar da suke samu kan ’yan bindiga, da ’yan ta’adda da masu satar mnutane a fadin Najeriya,” in ji shi.

Lai Mohammed wanda Babbar Daraktar Sashin Kula da Al’adu ta ma’aiktar, Memunat Idu-LAh, ta wakilta, ya ce tuni gwamnati ta aike da kudurori biyu ga Majalisar Dokoki ta kasa, kan dakile yaduwar bama-bamai, da kananan bindigogi da sauran kananan makamai a hannun ’yan Najeriya.

“Haka kuma gwamnatin na hada hannu da sauran kasashen Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen  Yammacin Afirka (ECOWAS), domin kawo karshen matsalar tabarbarewar tsaro a NaJeriya,” in ji shi.

Kazalika ya ja hankalin ’yan jarida kan yada labaran karya da ka iya jawo tashin hankali, da tabarbarewar tsaro.

A nasa bangaren, babban sakataren cibiyar NICO, Ado Muhammad Yahuza, ya ce taron an shirya shi ne sabdoa muhimmacnin raya al’ada ga cigaban kasa, kuma ’yan jarida na cikin wadanda za su taka muhimmar rawa wajen cimma hakan.

“Duk shekara muna shirya makamancin wannan taron, da masu ruwa da tsaki domin sanin al’adun da ke tafiya kafada da kafada da samun zaman lafiya a tsakanin kowacce al’umma.