✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bayan wasanni 18 an doke Akwa United a Firimiyar Najeriya

Tun daga watan Fabrairu, babu wata kungiya da ta yi nasara a kan Akwa United.

Katsina United ta kawo karshen wasanni 18 da Akwa United ta buga ba tare da an yi galaba a kanta ba a gasar Firimiyar Najeriya.

Tun daga ranar 14 ga watan Fabrairun bana, babu wata kungiya da ta yi nasara a kan Akwa United wacce take ci gaba da zama a saman teburin Firimiyar Najeriya a mako na 29.

Tun gabanin tafiya hutun rabin lokaci, Katsina United ta samu nasara kan Akwa United yayin wasan da suka fafata a filin Muhammadu Dikko da ke Jihar Katsina.

Kwallon da Samuel Kalu ya jefa tun a minti na 15 a bugun daga kai sai mai tsaron raga ita ce kwallo daya tilo da ta raba gardama a wasan a yayin da yaran Kennedy Boboye suka kwashi kashinsu a hannu karo na hudu kenan a kakar wasanni ta bana.

Kafin ziyarar da Akwa United ta kai wa Katsina United, a makon da ya gabata ne ta lallasa Adamawa Uniteda da ci biyu da nema.

Sai dai duk wannan sakamako, Akwa United ta ci gaba da zama a saman teburin Firimiyar Najeriya da maki 53 cikin wasanni 29 da ta buga.

Nasarawa United da Kano Pillars ne suka biyo bayanta a mataki na biyu da na uku inda kowacce take da maki 52.

A filin wasa na Lafia Township ne Nasarawa United ta samu nasarar lallasa Rivers United da ci 2-1, inda ita kuma Pillars ta yi wa Ifeanyi Ubah ci daya mai ban haushi a filin wasa na Sani Abacha.

David Ebuka ne ya jefa wa Pillar kwallonta daya tilo a wasan yayin da Ahmed Musa ya taimaka masa daga bugun kusurwa a minti na 27.

Wannan ita ce nasara karo na 16 da yaran Ibrahim Musa suka samu a kakar gasar Firimiyar Najeriya ta bana.

A filin wasan na kasa da kada da ke birnin Jos, Plateau United ta ci gaba da tsawaita kare martabarta zuwa wasanni 14 ba tare da an doke ta a gidanta ba bayan ta rike Enyimba babu ci.

Kungiyoyin biyu bayan buga wasanni 28 a gasar Firimiyar, suna mataki na hudu da na biyar inda kowanensu ke da maki 48.

Ga yadda sakamakon mako na 29 da aka buga ranar Lahadi a gasar Firimiyar Najeriya ya kasance:

Wikki Tourists 1-0 Lobi Stars

Abia Warriors 0-1 Dakkada FC

Heartland FC 2-0 MFM FC

Kano Pillars 1-0 FC Ifeanyi Ubah

Katsina United 1-0 Awka United

Kwara United 1-0 Sunshine Stars

Nasarawa United 2-1 Rivers United

Plateau United 0-0 Enyimba International

Warri Wolves 0-1 Rangers International