✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bayan wata 11 cikin duhu, an dawo da wutar lantarki a Maiduguri

Lamarin dai ya tilasta wa masu kananan sana’o’i neman wasu hanyoyin samun kudi.

Mazauna wasu sassa na Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, sun shiga cikin farin ciki saboda dawo musu da wutar lantarki bayan shafe wata 11 a cikin duhu.

An jefa birnin ne cikin duhu sakamakon hare-haren da ’yan Boko Haram suka kai wa wasu hanyoyin wutar lantarki da ke kaiwa ga birnin.

Aminiya ta gano cewa lamarin dai ya yi matukar gurgunta masu kananan sana’o’i tare da tilasta wa jama’a da dama komawa amfani da injinan janareta don samun lantarkin.

An dai fara dawo da wutar ne yankin Bulunkutu, ranar 22 ga watan Disamba, kafin daga bisani a dawo da ita a yankin Pompamari, da ke cikin birnin.

Mazauna birnin, musamman matasa masu kananan sana’o’i irinsu canjin waya, wanki da guga da aski da sayar da lemuka da kuma kankara da masu sayar da ruwa da ma yara, na daga cikin wadanda suka yi farin cikin sake dawowar wutar.

Gwamnatin Jihar ta Borno dai ta tallafa wajen kokarin sake dawo da wutar ta hanyar sake hada birnin da hanyoyin lantarkin da suka taso daga Damaturu, babban birnin Jihar Yobe.

Aminiya ta gano cewa ’yan ta’addan sun yi ta lalata kayayyakin lantarkin a baya, lamarin da ya kawo tsaiko wajen aikin sake dawo da ita a birnin.

Wani mazaunin unguwar  Bulunkutu Kasuwa, Ibrahim Ali, ya shaida wa wakilinmu cewa dawo da wutar ya sa farin cikin a zukatan jama’a, musamman masu sana’o’in hannu, masana’antu, ’yan kasuwa da masu injinan nika.

Ya ce, “Mun samu kiraye-kirayen waya da dama a kan dawowar wutar. Wasu abokanmu ina iya tunawa sun kirani don su tabbatar ko gaskiya ne, wannan kamar wani bakon abu ne.

“Muna farin ciki matuka, na tabbatar yanzu masu sana’o’i da dama za su dawo, mutane za su samu sa’ida.

“Wutar sai da ta yi kusan kwana biyu kafin a dauketa, amma yanzu kusan kullum ma ake kawowa. Yanzu Alhamdulillah, a baya an jefa mu cikin duhu ba gaira ba dalili,” inji shi.

Shi ma wani mazaunin yankin, Ahmed Modu, ya ce dawo da wutar ya kawo musu cikakkiyar natsuwa yanzu.

Binciken da wakilinmu ya gudanar ya gano cewa masu kananan sana’o’i ne lamarin ya fi shafa, yayin da da yawa daga cikinsu tilas suka rurrufe wurarensu, musamman masu sana’ar kafinta da walda da kuma wayarin din wuta.

Akasarinsu dai sun koma neman wasu sana’o’in, sakamakon suna bukatar manyan injinan janareta kafin su iya yin aiki.

Kazalika, kanana da matsakaitan masana’antu da dama su ma sun rufe a birnin na Maiduguri, lamarin da ya haddasa tashin farashin kayayyaki.

Bugu da kari, da yawa daga cikin irin wadannan masana’antun kuma sun kori wasu ma’aikata, wasu da dama kuma an kulle su.

Hakan ya kuma sa ’yan kasuwa masu sayar da injinan janareta sun kara masa kudi sosai.