✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Bayern Munich ta dauki Nagelsmann a matsayin sabon kocinta

Bayern Munich ce ke saman teburin gasar Bundesliga ta bana da maki 71 cikin wasanni 31 da ta buga.

Kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich ta tabbatar da kulla yarjejeniyar daukar kocin RB Leipzig, Julian Nagelsmann.

Sabon kocin zai karbi ragamar horas da kungiyar daga ranar 1 ga watan Yuli, 2021.

Munich ta dauko Nagelsmann a kan kudi €25, bayan warware yarjejeniyar da kocinta, Hansi Flick ya yi.

Nagelsmann mai shekaru 33, zai jagoranci kungiyar ne sakamakon kokari da bajintar da ya yi a kungiyar RB Leipzig.

Bayern Munich wacce ta lashe gasar Bundesliga har sau 29 a tarihi, a yanzu ita ce ke saman teburin gasar ta bana da maki 71 cikin wasanni 31 da ta buga.

RB Leipzig ita ce a mataki na biyu a teburin gasar da maki 64.