✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bayern Munich ta jefa Arsenal a tsaka mai wuya

A shekaranjiya Laraba ne aka yi wasa a tsakanin kulob din Bayern Munich da ke Jamus da kuma na Arsenal da ke Ingila a cigaba…

A shekaranjiya Laraba ne aka yi wasa a tsakanin kulob din Bayern Munich da ke Jamus da kuma na Arsenal da ke Ingila a cigaba da gasar zakarun kulob-kulob na Turai (UEFA Champions League) wasa karo na hudu.

A wasan, Munich ce ta yi wa Arsenal luguden kwallaye har biyar yayin da Arsenal ta jefa kwallo daya tilo inda aka tashi wasan 5-1.
Yanzu Munich ce ke kan gaba a rukunin da maki 9 yayin da Olympiakos ke biye da ita da maki 9 sai Dinamo Zagreb da maki 3 yayin da Arsenal ma ke da maki 3 amma ita ce ta karshe saboda yawan kwallaye a tsakaninta da Zagreb.
Yanzu wasanni biyu suka rage a wasannin zagaye na farko a gasar, daga nan ne za a tantance kulob bibbiyu daga kowane rukuni wanda za su haura zagaye na biyu.
Wannan ya nuna tilas sai kulob din Arsenal ya samu nasara a sauran wasanni biyun da suka rage masa don ya hada amaki 9, kuma duk da haka ya danganci yawan kwallayen da zai zura a raga don ya samu damar hayewa zagaye na gaba, amma ko kunnen doki kulob din ya yi a wasa na gaba, babu makawa an fitar da shi daga gasar kenan.
Kulob din da suka samu nasarar hayewa zagaye na gaba a gasar duk da saura wasanni biyu a kammala zagayen farko su ne na Real Madrid da ke Sifen da na Manchester City na Ingila da kuma na St. Petersburg na Rasha.
Kulob din FC Barcelona ne yake rike da kofin, bayan ya lallasa na Jubentus da ke Italiya a bara a wasan karshe.