✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bayern Munich ta zura kwallo 16 a wasa 4 da ta yi da Barcelona

Bayern Munich na daya daga cikin kungiyoyin kwallon kafa a duniya da ke samun galaba a kan takwararta ta Barcelona a galibin lokacin suka hadu…

Bayern Munich na daya daga cikin kungiyoyin kwallon kafa a duniya da ke samun galaba a kan takwararta ta Barcelona a galibin lokacin suka hadu a wasannin Gasar Cin Kofin  Zakarun Turai.

Duk da irin kashe makudan kudin da Bracelona ta yi a wurin cefano ‘yan wasa, ciki har da dauko dan gaban kungiyar Bayern Munich, Robert Lawendoski, amma a hakan sai da Barcelona ta sha kashi a hannun Bayern Minich a wasan da suka buga na Gasar Cin Kofin Zakarun Turai a ranar Talata.

Kungiyar ta Bayern Munich dai ta zura kwallo 16 a ragar Barcelona a cikin haduwa hudu da suka yi na baya-bayan nan, a inda ita kuma Barcelonan ta zura kwallo biyu kacal a ragar Bayern Munich din a cikin haduwa hudu din da suka yi.

Haduwar farko a baya-bayan nan ita ce ta ranar 14 ga watan Agusta, 2020 a wasan dab da na kusa da karshe na gasar cin Kofin Zakarun Turai, da Bayern Munich ta tumurmusa Barcelona da ci takwas da daya (8-2).

Na biyu shi ne 14 ga watan Satumba, 2021.

A wasan Munich din ta cimma Barcelona har gidanta sannan kuma na saka mata kwallo uku a raga {0-3}.

Wasa na uku shi ne na ranar takwas ga watan Disamba, 2021.

A wannan wasan Barcelona na neman samun nasara domin fitowa daga gurbin Gasar Cin Kofin Zakarun Turai, sun je a gidan Bayern Minich da zummar gwada samun nasara a kansu sai dai hakan bai samu ba, saboda a wasan ma Barcelona ta sake shan kashi a hannun Bayern Munich kamar yadda ta saba, an tashi ci uku da babu {3-0} in Bayern din ta zura kwallo uku a ragar Barcelona hakan kuma ya sa Barca din ta koma buga wasannin Gasar cin Kodin Urofa.

Na hudun shi ne ranar 13 ga watan Satumba, 2022.

A wannann makon ne aka buga wasan rukunin ‘C’ da aka sake hada Barcelona da Bayern Munich  a gurbi daya, duk da irin cefane da Barcelona din ta yi sai da ta sake shan kashi a hannun kungiyar Bayern Munich.

A wasan an tashi ci biyu da babu (2-0).

Idan aka hada wadannan kwallayen da Bayern Munich ta zura a ragar Barcelona to za a samu adadin kwallo 16 da ta zura a cikin wasanni hudu da suka hadu na baya-bayan nan a wasanin Gasar Cin Kofin Zakarun Turai.