✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bene mai hawa biyu ya rufta kan mutane a Abuja

Wani bene mai hawa biyu da ake kan ginawa ya rufta kan masu aikii a Garin Kubwa na yankin Birnin tarayya Abuja. Lamarin ya faru…

Wani bene mai hawa biyu da ake kan ginawa ya rufta kan masu aikii a Garin Kubwa na yankin Birnin tarayya Abuja.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 11 da rabi na daren Alhamis kamar yadda Aminiya ta samu labari.

Tuni dai aka kubutar da mutum biyar daga cikin ’yan aikin tun a daren, tare da garzayawa da su zuwa asibiti, a yayin da ake ci gaba da neman ragowar mutum biyu zuwa lokacin da wakilinmu ya isa wajen.

Wani daga cikin wadanda aka kubutar din mai suna Hafeez Solayinka da ya ce sun fara aikin bangarensu ne a Ranar Litinin da ta gabata, ya ce akwai ragowar mutum biyu da ba a kai ga fitar da su ba, a bangaren gidan saman da suke kwance.

Ya ce ginin ya rufta a kansu ne a lokacin da suke kwance a cikin ginin da suke kwana bayan tashi daga aiki.

“Bayan faruwar lamarin mun duba ta inda alaman haske yake muka rarrafa, sai muka ji maganganun jama’a aka fitar da mu, in ji shi.

 

Wani makwabcin wajen mai suna Emmanuel Omoke ya shaida wa Aminiya cewa alamu sun nuna ginin na shirin rushewa tun kafin ranar da abin ya faru.

Emmanuel ya ce da farko an fara aikin wajen ne a matsayin kasuwar zamani, kafin aka sauya tsarin hawansa na daya da na biyu zuwa tsarin gida mai dakuna biyu da uku, kowanne a hade da falo.

Ya ce bayan faruwar lamarin a daren na Alhamis su makwabta ne suka fara gudanar da aikin ceton kafin jami’an hukumar kashe gobara da kuma jami’an tsaro su kai dauki.

A nasu bangaren, jami’an hukumar kai agajin gaggawa wato NEMA sun garzaya wajen a safiyar Juma’a nan inda suke ci gaba da gudanar da aikin ceton ta hanyan amafani da motar tono da kuma kwashe kasa wato buldoza.

Babban Jami’in Hulda da Jama’a na hukumar ta NEMA, Manzo Ezekiel, ya tabbatar da cewa mutum 7 ne suka samu labarin ke cikin ginin a lokacin da lamarin ya faru.