✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bene ya rushe ya danne masu aikin gina shi a Taraba

Sai dai Aminiya ta lura rashin ingantattun kayan aikin ceto na matukar kawo tarnaki

Ana fargabar mutane da dama sun mutu bayan wani ginin bene ya rushe ana tsaka da aikin gina shi a Jalingo, babban birnin Jihar Taraba a ranar Juma’a.

Aminiya ta gano cewa ginin wanda ake cikin aikin shi, ya rushe ne a lokacin da ma’aikata ke cikinsa.

Tuni dai aka fara tono gawarwakin mutane da dama, yayin da wasu kuma baraguzan gini sun danne su.

Ginin, wanda ke kusa da Kwalejin Fasaha ta Jihar Taraba, an ce mallakin wani hamshakin dan kasuwa ne mai harkar sayar da kayan gini.

Lamarin dai ya tunzura ’yan uwan leburorin inda suka fara gudanar da wata zanga-zanga a kai.

Sai dai binciken Aminiya ya gano cewa rashin ingantattun kayan aikin ceto na matukar kawo tarnaki ga aikin ceto wadanda ginin ya danne, inda mutanen unguwa ne suke ta aikin, yayin da aka tsaurara matakan tsaro a yankin.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, DSP Usman Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce tuni aka tono gawarwakin masu aikin ginin mutum uku, yayin da kuma ake ci gaba da aikin ceton.