✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Beraye sun fatattaki fursunoni daga gidan yari

Ana fama da annobar beraye kusan duk bayan shekara goma a yankin.

Matsanancin buruntu da beraye ke yi ya sa an sauya wa fursunoni matsugunni daga wani gidan cin sarka a Kasar Australiya bayan sun addabe su.

Kwamishinan Hukumar Kula da Gidajen Yari na Kasar, Peter Severin wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Talata, ya ce berayen sun tilasta kwashe fursunonin da suka hada da mata da maza daga gidan yarin zuwa wasu.

Fursunoni 420 da ma’aikata 200 na gidan yarin Wellington da ke New South Wales aka sauya wa matsugunnin na tsawon mako biyu gabanin a yi maganin berayen.

Bayanai sun ce berayen sun yi barna gaya inda suka lalata gidan yarin sannan sun cinye wayoyin lantarki.

Kasar Australiya dai tana fuskantar annobar beraye kusan duk bayan shekara goma inda suke addabar al’umma, gami da lalata amfanin gona.

Wasu manoma a kasar sun ce suna kama akalla beraye 500 zuwa 1000 duk rana, yayin da mazauna kasar suka shaida wa jaridar Washington Post cewa suna fama da hamamin berayen da suka mutu suka rube a cikin garun gidajensu.