✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Beraye sun mamaye kwalejin ‘Ramat Poly’ —Zulum

Gwamnan Borno ya dakatar da shugabannin kwalejin na tsawon wata shida.

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, ya dakatar da hukumar gudanarwar Kwalejin Kimiyya da Kere-kere ta ‘Ramat Poly,  da ke Jihar saboda beraye da suka mamaye kwalejin.

Zulum ya dakatar da shugabannin kwalejin ne na tsawon wata shida, lokacin ziyarar da ya kai ranar Talata, ya samu dakunan gwaje-gwaje da na koyon gyara da koyon sana’o’i na kwalejin ba sa aiki, beraye da yanar gizo-gizo duk sun mamaye su.

“Na umarci Kwamishinan Ilimi Mai Zurfi da Kimiyya da Kirkira, Dokta Babagana Mallumbe, ya karbe ragamar shugabancin kwalejin nan take daga yanzu zuwa wata shida masu zuwa; kuma ma’aikatarsa ta tabbatar cewa ta gyara dakunan gwaje-gwajen sun ci gaba da aiki nan take.

“Dakin koyon sana’o’i kuma a tabbata an farfado da shi nan take ya ci gaba da aiki; Lokacin da nake shugaban kwalejin nan, a kowane wata kujeru da bencinan makaranta 10,000 zuwa 20,000, baya ga gadajen asibiti da muke yi,” inji shi.

Sanarawar da kakakin gwamnan, Isah Gusau ta fitar ta ce “A lokacin ziyarar, Gwamnan ya samu an yi watsi da akasarin dakunan gwaje-gwaje ba sa aiki, beraye da yanar gizo-gizo sun mamaye su.”

Gwamna ya ce, “Abin da na gani ya nuna kwalejin ya mutu murus babu abin da yake aiki; Dakunan gyaran injina da na koyon sana’a da ayyukan gona duk sun mutu.

“Sannan matsaloli sun dabaibaye kwalejin saboda rashin isassun kudade da kuma rashin bayar da himma.

“A matsayina na tsohon dalibi kuma tsohon shugaban wannan kwaleji dole in shigo ciki; In Allah Ya yarda ba zan bari ta durkushe ba, a matsayina na Gwamnan Jihar Borno, zan yi duk abin da ya kamata domin ganin ta dawo cikin hayyacinta.”