✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bethel Baptist: Dalibai 121 ke hannun mu — ’Yan bindiga

Mun samu damar tattauna wa da wasu daga cikin daliban.

’Yan bindigar da suka kai hari makarantar sakandaren Bethel Baptists High School da ke Kudancin Jihar Kasuna, sun ce dalibai 121 ne ke hannu su.

Shugaban makarantar, Rabaran Yahaya Adamu Jangodo, ne ya tabbatar da hakan yayin ganawa da manema labarai a ranar Talata bayan maharan sun tuntube su.

Ya ce ’yan bindigar sun tabbatar da cewa dukkan daliban da ke hannunsu na cikin koshin lafiya.

Jangodo ya ce sun kuma gana da wasu daga cikin daliban da aka sace yayin da ’yan bindigar suka tuntube su, idan suka tabbatar da hakikanin adadinsu da ke tsare kamar yadda maharan suka zayyana.

“A ranar Talata cikin yardar Allah mun tattauna da ’yan bindigar da suka kira ta waya kuma sun tabbatar mana da cewa daliban suna cikin koshin lafiya.

“Mun samu damar tattauna wa da wasu daga cikinsu kuma sun tabbatar mana da koshin lafiyarsu.

“Sun ce an kidaya su kuma an samu adadin dalibai 121 da ke tsare, wanda hakan ya yi daidai da alkaluman daliban da muka tabbatar an sace daga dakunansu na kwana,” a cewarsa.

Jangado ya ce sun shaida wa iyayen daliban halin da ake ciki kuma sun yi musu godiya kan juriyar da suka yi a cikin wannan mawuyacin hali.

Ya nemi iyayen da su kwantar da hankalinsu domin kuwa gwamnatin Jihar Kaduna na sane da halin da suka ciki kuma za ta yi duk wata mai yiwuwa domin kubutar da ’ya’yansu.

Aminiya ta ruwaito cewa, a safiyar Litinin da ta gabata ce ’yan bindigar suka kai hari makarantar kwanan ta maza da mata da ke kan babbar hanyar Kaduna zuwa Kachia, inda suka kwashi dalibai da dama.

Bayanai sun ce sojoji biyu sun rasa rayukansu yayin musayar wuta da ’yan bindigar da suka kai harin.