✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Biden ya karyata Zelensky kan harin Poland

Kasashen da suka yi wa Rasha ca sun yi shiru bayan an gano Ukraine ce ta harba makamai masu linzami zuwa Poland

Shugaban Kasar Amruka, Joe Biden, ya karyata ikirarin Shugaban Kasar Ukraine, Volodymyr Zelensky, da ke cewa harin makamai masu linzami da aka kai wa Poland ba daga Ukraine ba ne.

Da farko an zargi Rasha, wadda ke yaki da Ukraine da harba makaman zuwa Poland, har jijiyoyin wuya suka tashi, amma Rasha ta nesanta kanta da harin.

Daga bisani gwamnatin Poland ta ce makaman sun shigo kasarta ne daga Ukraine, wanda ya sa kasashen da suka yi wa Rasha ca, suka sassauta.

Zargin na zuwa ne bayan harin makamai masu linzami daga Rasha sun ragargaza cibiyoyin iskar gas da wasu muhimman kayan more rayuwa na Ukraine.

A yayin da ake wannan dambarwa, an kasa cim-ma yarjejeniya kan batun fitar da sinadarin ammonium na Rasha zuwa kasuwar duniya.

Wata majiya ta ce an kasa cim-ma daidaita kan ammonium na Rasha mai matukar muhimmanci, wanda take fitarwa ta bututun da ya rasa ta Bahar Maliya.

Hakan ta taso ne a yayin da ake kokarin sabunta jarjejeniyar fitar da hatsi daga Ukraine zuwa kasuwannin duniya.