✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Biden ya sake yi wa Trump fintinkau a zaben Amurka

Joe Biden ya sake yi wa shugaba mai ci kuma dan takarar jam’iyyar Republican, Donald Trump fintikau

Dan takarar jam’iyyar Democrat a zaben Amurka, Joe Biden ya sake yi wa shugaba mai ci kuma dan takarar jam’iyyar Republican, Donald Trump fintikau bayan an tattara sakamakon jihohin Pennsylvania da Georgia masu matukar muhimmanci.

Ya zuwa yanzu dai, a cikin kuri’u sama da 30,000 da aka sake sanarwa, Biden ya lashe sama da kaso 87 cikin 100 nasu.

Lashe jihar Pennsylvania dai zai ba duk wanda ya sami nasara samin karin kuri’u 20 daga kwalejin zabe wanda zai ba shi damar zama shugaban kasa.

Wannan dai shine sakamakon da ya fi kowanne yawan kwalejin zaben daga cikin dukkan jihohin masu muhimmanci da ba a kai ga bayyana sakamakonsu ba.

Hakan dai na iya ba Biden damar samun sama da kuri’u 270 na kawalejin da yake bukata domin lashe zaben.

Shugaba Trump dai na cikin tsaka mai wuya la’akari da yadda lokaci ke kara kure masa wajen ganin ya kamo tazarar da Biden ya yi masa.

Jami’an zaben dai sun ce ana aiki ba dare ba rana wajen tattarawa da kuma kirga dukkan kuri’un da aka kada a jihohi, inda suka ce kirga wadanda aka aika ta imel ne ke kawo tsaiko.

A lokuta da dama dai shugaba Trump ya yi zargin cewa an tafka magudi a zaben, lamarin da ya sa har sai da shafukan sada zumunta na Twitter da Facebook suka rika taka masa birki saboda gudun yada labaran karya.