✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Biden ya yaba da yarjejeniyar tsagaita wuta a yakin Isra’ila da Falasdinawa

An fara tsagaita wutar ranar Juma'a, wanda ya kawo karshen kwana 11 ana gumurzu.

Shugaban Amurka, Joe Biden, ya yaba da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas a Zirin Gaza tare da jaddada cewa Amurka za ta ci gaba taimaka wa Isra’ila ta fuskar soji.

Biden ya bayyana farin cikinsa ne cikin jawaban da ya yi a Fadar White House da ke Washington DC, a yayin da yarjejeniyar tsagaita wutar ta fara aiki da safiyar Juma’a a Gaza.

Sanarwar ta ce, “Amurka za ta ci gaba da goyon bayan Isra’ila wajen kare kanta daga hare-haren Hamas da sauran kungiyoyi ta’adda da ke Gaza wadanda suka janyo salwantar rayukan mutanen da ba su ji ba kuma ba su gani ba.

“Wadannan hare-hare sun janyo mutuwar fararen hula da dama ciki har da kananan yara, sannan ina mika sakon ta’aziyyata ga duk Isra’ilawa da Falasdinawan da suka rasa ’yan uwansu,” a cewar Biden.

A wata ganawa ta wayar tarho da Biden ya yi ranar Alhamis tare da Firaiminista Benjamin Netanyahu, ya yaba wa Isra’ilawa kan tsagaita wutar wadda a cewarsa, zai bayar da wata dama ta samun ci gaba a fagen zaman lumana.

Haka kuma, ya yi wata ganawa da Shugaba Abdel Fattah el-Sisi na Kasar Masar da kuma Shugaban Falasdinawa, Mahmoud Abbas, inda ya yaba musu dangane da yarjejeniyar diflomasiyya da suka kulla wajen ganin an tsagaita wutar.

Shugaban na Amurka ya yi godiya gami da jinjina ga takwaransa na Masar a kan shiga da fitar da ya yi wajen cimma wannan yarjejeniya tsakanin Isra’ila da Hamas.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa, an fara tsagaita wutar ne da sanyin safiyar Juma’a, wanda ya kawo karshen kwana 11 ana jefa bama-bamai da suka yi sanadin mutuwa fiye da mutum dari biyu.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa, Kasashen Masar da Qatar da kuma Majalisar Dinkin Duniya ne suka yi ruwa da tsaki wajen cimma yarjejeniyar tsakanin Isra’ila da Hamas, wadda ke iko da birnin Gaza.