✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Biden ya zabi Shugaban Ma’aikatan Fadar White House

Shugaban Amurka mai jiran gado, Joe Biden, ya nada Ron Klain a matsayin Shugaban Ma’aikatan Fadar White House. Sanarwa da kwamitin karbar mulki na Biden…

Shugaban Amurka mai jiran gado, Joe Biden, ya nada Ron Klain a matsayin Shugaban Ma’aikatan Fadar White House.

Sanarwa da kwamitin karbar mulki na Biden ya fitar a ranar Laraba, ta ce Ron zai jagoranci kula da al’amuran da suka shafi ofishin Shugaban Kasa a matsayinsa na babban mashawarci.

“Baya ga goyon bayan zababben Shugaban, Mista Klain zai yi aiki don kafa wata tawagar hazikan mutane don taimaka wa Zababben Shugaba Biden da Mataimakiyarsa Kamala Harris su tunkari kalubalen da kasar ke fuskanta”, inji sanarwar.

Mista Biden ya ce: “Ron ya kasance mai matukar muhimmanci a wurina tsawon shekarun da muka yi aiki tare, musamman yadda muka ceto tattalin arzikin Amurka daga cikin mawuyancin hali a 2009 sannan muka shawo kan wata babbar matsalar lafiyar al’umma a 2014.

“Zurfin tunaninsa da gogewa a kan aiki da mutane a bangarorin siyasa daban-daban shi ne ainihin abin da nake bukata daga Shugaban Ma’aikata na Fadar White House a yayin da kasarmu ta ke fuskantar kalubale iri-iri”.

Dangane da nadin nasa, Mista Klain ya ce: “Abin karamci ne a gare ni in yi wa zababben Shugaban Amurka hidima a wannan mukamin kuma amincewarsa da ni ya zamto abin alfahari a gare ni.

“Ina fata tare da zummar taimaka masa da mataimakiyarsa wajen hada karfi da karfe don yin aiki a White House yayin da muka fuskanci manufofinsu na kawo managarcin sauyi da karshen bambance-bambance a kasarmu”, inji shi.

Mista Klain Babban Mashawarci ne a Kwamitin yakin neman zaben Mista Biden kuma a baya ya yi wa zababben shugaban kasar ayyuka da dama ciki har sa Shugaban Ma’aikatansa a lokacin da yake Mataimakin Shugaban Kasa.

Mista Klain ya shahara musamman saboda da rawar da ya taka a matsayin Babban Jami’in Fadar White House mai kula da yaki da cutar Ebola

Nadin Mista Ron na zuwa ne duk da ki fadin da Shugaba Donald Trump ya yi na amince wa da sakamakon zaben da aka gudanart a ranar 2 ga watan Nuwamba.