✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bidiyon Dala: Ganduje da Jaafar Jaafar sun hadu a London

An ga Ganduje da Jaafar Jaafar cikin sakin fuska da raha, har suka rungume juna a lokacin haduwar tasu a London

Dan jaridar nan da ya fitar da bidiyon zargin Gwamna Abdullahi Ganduje na Jihar Kano da karbar  daloli a matsayin cin hanci, Jaafar Jaafar ya hadu gwamnan a kasar waje.

A ranar Litinin Jaafar Jaafar, mawallafin jaridar Daily Nigerian, ya wallafa bidiyon haduwarsu da Ganduje a birnin London na kasar Birtaniya.

Duk da takaddamar da ke tsakaninsu, a karon farko, a bidiyon, an ga Gwamnan Ganduje da Jaafar Jaafar kowannensu cikin sakin fuska da raha, suka sha hannu, sannan suka rungume juna.

Hakan ta kasance ne a harabar Chatham House, inda dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC, Bola Tinubu ya je gabatar da jawabi a ranar.

Ganduje wanda dan ga-ni-kashe-nin Tinubu ne, yana cikin manyan ’yan Jam’iyyar APC da suka raka dan takarar zuwa Chatham House, inda a nan suka sake haduwa da dan jaridar.

Dambarwar bidiyon Dala

A shekarar 2018, kafofin Daily Nigerian mallakar Jaafar Jaafar suka fitar da wani bidiyo — da ya tarar da kura — wanda a ciki aka ga wani wanda dan jaridar ya ce Ganduje ne, yana karbar daloli yana cusawa a aljihu.

Dan jaridar ya yi zargin cewa gwamnan ne a bidiyon a lokacin da yake karbar cin hanci a kudin Dalar Amurka daga wani dan kwangila da Gwamnatin Jihar Kano ta ba wa aiki — zargin da gwamnan ya sha karyatawa.

Daga bisani Ganduje, wanda ya ce an yi wa bidiyon suddabaru ne, ya maka Jaafar Jaafar a kotu, yana neman diyyar Naira biliyan uku kan zargin bata masa suna.

Gwamnan ya kuma ce ya kafa kwamiti domin gudanar da bincike kan bidiyon da masu hannu a ciki.

Har yanzu shari’ar na gaban kotu, a yayin da Jaafar ya koma kasa waje, tare da cewa ana yi wa rayuwarsa barazana kan bidiyon da ya fitar.