✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bidiyon Dala: Kotu ta fitar da ranar ci gaba da shari’ar Ganduje

Ganduje ya bukaci sauya wasu daga cikin shaidun da za su kare shi a gaban kotun.

Wata Babbar Kotu a jihar Kano ta tsayar da ranar takwas ga watan Maris, 2021 a matsayin ranar da za a ci gaba da sauraren karar da ake zargin Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje da karbar cin hanci.

Tun ranar 10 ga Nuwanbar 2020, Ganduje ta hannun lauyansa ya bukaci kotun ta ba shi dama don sauya wasu daga cikin shaidun da za su ba da shaida a kansa a gaban kotu.

A karshen shekarar 2018 ne dai jaridar nan ta intanet mai suna Daily Nigerian ta Ja’afar Ja’afar ta wallafa wasu faya-fayan bidiyo da aka ga gwamnan yana karbar wasu makuden Daloli da ake zargin cin hanci ne yana zuba wa a aljihu, ko da yake dai ya sha musanta sahihancinsu.

Tuni lauyan Jafar Jafar, U.U. Etem ya soki bukatar gwamnan kan gabatar da shaidun, inda ya ce ta saba da dokar kotun.

Sai dai lauyan Ganduje ya dage kan cewa bukatar ba ta saba da doka ta 24, karkashin sashi na 1, 2, da 3 na shekarar 2014 ba.

Daga nan alkalin kotun, Mai Shari’a Suleiman Baba Namalam ya dage zaman kotun har zuwa takwas ga watan Maris na 2021 domin ci gaba da sauraron karar.

Idan za a iya tunawa Daily Nigerian ta fitar da jerin faya-fayan bidiyon wadanda a cikinsu ta yi zargin kudaden da Gandujen ya karba sun kai kimanin Dala miliyan biyar a aljihun babbar rigarsa.

Sai dai tun a wancan lokacin, gwamnan ya yi watsi tare da karyata bidiyon da aka yada inda ya bayyana shi a matsayin sharrin ‘yan adawa.