✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bidiyon fallasa: Kotu ta kori karar da aka kai Ganduje

Wata Babbar Kotun Jihar Kano ta yi watsi da karar da aka shigar gabanta kan zargin da ake yi wa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na…

Wata Babbar Kotun Jihar Kano ta yi watsi da karar da aka shigar gabanta kan zargin da ake yi wa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar na karbar cin hanci da rashawa da aka fallasa a bidiyo, saboda rashin gamsassun hujjoji.

A kwanakin baya ne wani lauya mazaunin Kano Barista Bulama Bukarti, ya shigar da karar inda ya bukaci Babbar Kotun ta bai wa Hukumar EFCC izinin binciken Gwamna Ganduje a bidiyon da yake nuna Gwamnan na karbar daloli daga hannun wadansu ’yan kwangila. Idan za a iya tunawa a bara ce jaridar Intanet ta Daily Nigerian ta wallafa wani bidiyo da ke nuna Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na karbar cin hancin Dala miliyan biyar daga hannun wadansu ’yan kwangila. Bidiyon dai ya jawo cece-ku-ce da musayar kalamai, inda gwamnatin Kano ta zargi Editan jaridar Daily Nigerian Ja’afar Ja’afar da yunkurin bata sunan Gwamna Ganduje ta hanyar wallafa biyon da ba ya da sahihanci.

Hukuncin kotun zai dakatar da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) game da binciken da ake yi wa Gwamna Ganduje kan karbar cin hanci daga hannun ’yan kwangila.