✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bidiyon Fallasa: Kotu ta yi watsi da shari’ar Ganduje

Wata babbar kotun jihar Kano ta yi watsi da karar da aka shigar gabanta game da zargin da ake yi wa gwamna Abdullahi Umar Ganduje…

Wata babbar kotun jihar Kano ta yi watsi da karar da aka shigar gabanta game da zargin da ake yi wa gwamna Abdullahi Umar Ganduje na karbar hanci da aka fallasa a bidiyo.

Umarnin kotun zai dakatar da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) game da binciken da ake yi wa Gwamna Ganduje kan karbar cin hanci daga hannun ‘yan kwangila.

A kwanakin baya ne wani Lauya mazaunin Kano Barista Bulama Bukarti, ya bukaci kotun ta bai wa Hukumar EFCC izinin binciken Gwamna Ganduje a bidiyon da yake nuna Gwamnan na karbar daloli daga hannun wasu ‘yan kwangila.