Bidiyon fyade: An tsare dan hadimin Tambuwal a kurkuku | Aminiya

Bidiyon fyade: An tsare dan hadimin Tambuwal a kurkuku

    Nasiru Bello, Sakkwato

Kotu ta tsare dan wani mashawarcin Gwamnan Sakkawato, Aminu Tambuwal a kurkuku bisa zargin yada bidiyon tsiraicin wata budurwa.

Alkalin Kotun Majistare ta 1 a Sakkwato, Shu’aibu Ahmad ya umarci a tsare Baffa a kurkuku na sati biyu, kafin ci gaba da sauraron shari’ar.

Umarnin ya biyo bayan bukatar dan sanda mai gabatar da kara ASP Samuel Sule, na samun damar kammala bincike kan tuhumar da matashin ke fuskanta.

Samuel ya ce hakan zai ba da damar samun shawarar Babban Lauyan gwamnatin jihar saboda kotun ba ta da hurumin ci gaba da sauraron shari’ar fyade da ake wa matashin.

Ana zargin sa da yin fyade ga karamar yarinya da ya kai otel ba da yardar ta ba, nadar bidiyon da kuma fitar da shi a bayan shekara uku a lokacin da auren ta ya taso.

Fitar bidiyon ya yi sanadiyar janyewar maneminta daga batun auren baya ga jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin jama’a.

Baffa ya musanta zargin da ake yi masa a lokacin da alkali ya karanta masa abin da ake tuhumarsa a gaban kotu.

Alkali Shu’aibu ya kuma aminta da bayar belin abokan matashin su uku, duk da cewa na hudunsu ya dade da tserewa.

Ana zargin nsu da hada baki, ingizawa, bata suna da kuma sayar da littafin batanci, wanda hakan laifi ne a kundin dokar laifuka na Jihar Sakkwato.

Matasan sun ki amsa laifukan da ake zargin su da aikatawa, kuma har karshen zaman kotun ba a ga na biyar dinsu da ya tsere ba.

Kotun ta sanya ranar 19 ga Oktoba, 2020 domin ci gaba da sauraren karar.