✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bidiyon fyade: Gwamnatin Legas ta sake bude makarantar Chrisland

Sai dai gwamnatin ta ce za a ci gaba da bincike a kan lamarin

Gwamnatin Jihar Legas ta ba da umarnin sake bude makarantar Chrisland bayan rufe ta a baya sandiyar balahirar da ta biyo bayan sakin bidiyon badala tsakanin dalibanta masu kananan shekaru.

Lamarin dai ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin al’ummar kasar nan in da wasu ke Allah wadai da dora laifi ga iyaye da malaman yaran kan rashin ba su ingantacciyar tarbiya.

Gwamnatin dai a baya ta ba da sanarwar rufe dukkan rassan makarantar domin gudanar da bincike.

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da Kwamishinar Ilimi ta Jihar, Folasade Adefisayo, ta fitar inda ta ba da umarnin bude makarantar daga ranar Litinin mai zuwa.

Sanarwar ta ce umarnin ya biyo bayan binciken da gwamnati ke gudanarwa kan lamarin, da kuma tabbatar da ba a danne hakkin yara na neman ilimi ba, musammam ganin za su shiga sabon zangon karatu a ranar Litinin.

“Za Kuma a dinga bibiyar darussan makarantar daki-daki, musamman ziyarar karo ilimi na dalibai, domin kiyaye aukuwar hakan a nan gaba,” inji sanarwar.

Daga karshe gwamnatin ta ce za ta fitar da sabon daftarin koyarwa da tsare-tsaren makarantun kudi da na gwamnati a Jihar nan da wata guda.

A wani labarin kuma, Rundunar ’Yan Sandan Jihar ta ce tana ci gaba da binciken iyaye da ma’aikatan makarantar daliban da suka aikata badalar.

Aminiya ta gano wadannan mutanen na hannun Sashen Binciken Manyan Laifuka na rundunar domin ci gaba da bincike.