✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bidiyon masoya masu rungumar juna ya tayar da kura

Masoyan na rungumar juna a bainar jama'a bayan baikonsu a Kano.

Ana ci gaba da ce-ce-ku-ce kan wani sabon bidiyo da ya bulla a shafukan zumunta yana nuna wasu masoya na rawa da rungumar juna a bainar jama’a bayan yin baiko a Kano.

A cikin bidiyon na Instagram, an ga masoyan, saurayi da budurwa na rungumemeniya bayan saurayin ya saka mata zoben sa-rana a yatsarta.

https://www.instagram.com/tv/CCeOvWcA-Mz/?utm_source=ig_embed&utm_campaign=loading

Yawancin masu tsokaci dai a jihar da ma kafafen sada zumunta sun yi Allah-wadai da abun da matasan suka yi a bidiyon, suna masu cewa hakan ya saba da al’adu da addinan mutanen jihar.

A tattaunawarsa da Aminiya, wani sanannen malamin Musulunci a Kano Shaikh Nura Arzai ya yi tir da bidiyon yana mai cewa masoyan na kokarin kwaikwayon dabi’un Turawa ne wadanda suka saba da na al’ummar jihar.

Ko bayan an yi aure akwai ka’ida

Ya ce, “A Musulunce, lokacin da kawai ya halalta namiji ya taba mace shi ne lokacin da ya aure ta, shi ma ba a tsakiyar jama’a ba.

“Musulunci ya tanadi yadda za ka nemi aure; farko ka je wurin iyayenta ka nemi izini da kanka ko ta hanyar wakilci, in ka samu izinin sai ka fara neman yardarta, daga nan kuma in kun fahimci juna sai waliyyanka su je wajen nemanta da aure.

Bakuwar al’ada

“Abun da matasan suka yi wata bakuwar al’ada ce da suka aro daga mutanen Indiya da kuma Turawa.

“Abin takaicin shi ne mu Musulmai da muke da tsari, a maimakon mu zama abin kwaikwayo, sai matasanmu suka zama su suke kwaikwayon. Wannan abin takaici ne.

“Zuwan kafafen sa da zumunta na zamani duk sun canza komai. Ina kira ga matasanmu da musamman iyaye da su ci gaba da koyi da al’adunmu na Musulunci”, inji Sheik Nura Arzai.

Haramun ne

Babban Limamin Masallacin Juma’a na Triumph da ke Kano, Shaikh Lawal Abubakar ya ce, “Abun da suka yi haramun ne, Musulunci ya haramta koyi da dabi’un Yahudu da Nasara.

“Kuma Manzo (SAW) ya fada a cikin wani Hadisi cewa duk wanda ya yi koyi da wasu mutane to tabbas yana tare da su.

Tarbiya ta kara yin wuya

Shi kuwa a nasa bangaren, wani uba a Kano, Malam Haruna Adam ya koka cewa zuwan kafafen sada zumunta a sa sha’anin tarbiyya ya kara wahala.

“Na tabbata wannan daga wurin Turawa suka aro tunda dai ba mu da shi a addini ko al’adarmu. Ba na tunanin akwai wani uba mai hankali da zai so ya ga ana rungumemeniya da ‘yarsa kafin aure ya yi farin ciki”, inji Malam Haruna.

Wata uwa, Hajiya Lami Bello ta bayyana fargabar cewa sabon bidiyon na iya haifar da sabuwar sara da ‘ya’yansu za su fara kwaikwayo.

Irin abinda muke yaki da shi kenan – Hisbah

To sai dai babban kwamandan Hukumar Hisba ta jihar Kano, Muhammad Sani Ibn Sina yayi Allah-wadai da abinda matasan suka yi, yana mai cewa hukumarsa ta dade tana yaki da badala irin wannan.

Ya ce, “Wannan ya saba da addini da al’adarmu. Musulunci ya zayyana yadda neman aure ya kamata ya kasance, kuma babu wanda aka amince ya taba jikin mace ko ya saka mata zobe a danyatsa ba tare da aure ba.

“Ba wai kawai rungumemeniya ma suke a tsakiyar mutane ba, a’a mutanen har tafa musu suke suna murna alamar sun ji dadi, wannan abin Allah-wadai ne matuka.

“Ya kamata iyaye su ji tsoron Allah su san cewa ranar lahira za a tambayesu amanar ‘ya’yan da aka basu.

“Irin wadannan badalolin hukumarmu take yaki da su. Duk lokacin da muka samu irin wannan rahoton lallai ba za mu bari ba”, in ji babban kwamandan.