✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Bikin ‘Halloween’ a Saudiyya ya janyo cece-kuce

An yi bikin Halloween a Saudiyya.

An gudanar da bikin shigar dodanni na ‘Halloween’ a karon farko a Kasar Saudiyya, lamarin da ya janyo cece-kuce.

Bikin wanda asalinsa na turawa ne wanda ke da alaka da maguzanci na zamaninsu na jahiliyya, ya samu daurin gindin gwamnati a Saudiyyan

Rahotanni sun ce an soma shagulgulan bikin ne tun a ranar Alhamis, ana kuma sa rai za a kai ranar Litinin ana yi a Riyadh, babban birnin kasar.

Matasa maza da mata ne suka yi shigar dodanni da sauran shiga iri-iri ta ban tsoro, suka kuma fito kan titunan garin.

Hotuna da bidiyo na bikin ya karade intanet da kuma shafukan sada zumunta na yadda ake bikin har kwarya-kwayar shagalin casu na raye-raye da kade-kade irin na Turai aka yi.

Wannan shi ne karo na farko da aka yi wannan biki babu tsangwama da kama mutane, saboda a baya gwamnatin kasar ta hana bikin, tare da kama duk wanda aka gani musamman a shekarar da ta wuce.

Ra’ayin jama’a

Yawancin masu adawa da nuna rashin jin dadinsu ga bikin daga wajen kasar ne, wani mai suna Haruna Ali a shafinsa na Facebook, auziyya ya yi tare da kawo hadisin Manzo ﷺ da ke fadin bullar fitinu da girgizar kasa daga yankin Najd wato Riyadh a yanzu.

Shi kuwa wani mai suna Jibrin Ali cewa ya ke, lallai alkiyama ce ta zo, ganin yadda ake shigar shaidanu da kayan da suka fi soyuwa ga fiyayyen Halitta (SAW).

Shi kuwa Malam Yahuza Mohammad Salis wani malami a Abuja a hirar sa da Aminiya, danganta wannan lamari ya yi ga tasirin da Amurka ta yi a mulkin kasar, da kuma alkiblar Yarima Mohammad Bin Salman, la’akari da cewa wannan ba al’dar larabawa ba ce.

Asalin bikin Halloween

Bikin ya samo asali ne daga tatsuniyoyi ne na al’adar kabilun Turawa a zamaninsu na jahiliyya da maguzanci.

Ana bikin ne a kwanaki uku na karshen kowanne watan Oktoba ta kowacce shekara ta hanyar shigar dodanni da iskokai wadanda su ke fitowa domin a wannan lokaci don yin musharaka da dan Adam

Ana yin hakan ne a matsayin taya dodanni da iskokai murnar fita wata shekarar zuwa wata, a gargajiyarsu.

Sai dai abin da ya daurewa mutane kai shi ne yadda masu akidar kasar ke sukan bikin mauludi na fiyayyen Halitta amma suna bikin gargajiyar Turawa.