✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bikin Sallah: Za a girke jami’an tsaro 5,350 a Kwara

Za a girke su domin tabbatar aminci a yayin bukukuwan Sallah a Jihar.

Akalla jami’an tsaron 5,350 ne za a girke don tabbatar aminci a yayin bukukuwan Sallah Karama a Jihar Kwara.

Hadin gwiwar jami’an ’yan sandan da jami’an tsaron NSCDC, za a girke za su ne domin sanya ido kan manyan ababen hawa da kuma zirga-zirgar mutane a jihar.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, Ajayi Okasanmi ne ya sanar da hakan ga manema labarai, yayin tattaunawarsa da su a ranar Litinin.

Okasanmi, yayin da yake taya al’ummar Musulmi murnar Sallah Karama a jihar, ya ce hukuma ba za ta lamunci aikata laifuka daga bata-gari ba a yayin bukukuwan sallah.

Kazalika, Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadura (FRSC) reshen jihar, Jonathan Owoade ya shaida wa manema labarai cewa, hukumar ta su za ta girke jami’anta 1,500 da mototcin sintiri 40 don tabbatar da bin dokokin tuki a jihar.

Har wa yau, gamayyar kungiyar ’yan banga a jihar, za su girke dakarunsu har 1,500 a sassam jihar.