✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bikin shekara 60: Mun fi daukaka a dunkule —Buhari

Shugaba Buhari ya ce kasar za ta fi samun daukaka ne idan ta ci gaba da zama kasa daya

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce Najeriya za ta fi samun ‘daukaka’ idan dukkanin ’yan kasar suka ci gaba da kasancewa a ‘dunkule’ maimakon zama ‘daidaikun al’ummomi.’

Shugaban kasar ya fadi haka ne a cikin jawabinsa na Bikin Cika Shekara 60 da Samun ’Yanci.

Ya kuma yi nuni da muhimmancin kara himma tare da nuna juriya da yin abin da ya dace wajen gina kasar.

“Ya ’yan uwana ’yan Najeriya, idan har muna son cimma muradinmu, to akwai bukatar mu kara nuna juriya da kara azama wajen yin abin da ya kamata; ko da kuwa babu wanda yake ganinmu.

“Ya ’yan uwana ’yan Najeriya, lokaci ya yi da za mu kara dukufa domin ci gaba da zama tsintsiya madaurinki daya har fiye da shekara 60.

“Kuma a fili take cewa mun fi samun daukaka a lokacin da muke tare maimakon zama daidaikun al’ummomi daban-daban.

“Kuma da yardar Allah za mu ga bayan dukkan wani kalubalen da ke ci mana tuwo a kwarya.

“A yau, muna fuskantar dumbin matsalolin da suka addabi kasarmu mai yawan al’umma – fiye da mutum miliyan 200 da ke zaune a kasa guda – amma kashi 52 cikin 100 ke zaune a birane”, inji Shugaba Buhari.