✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

BIN DIDDIGI: Shin jarumar Bollywood Katrina Kaif Musulma ce?

Katrina Kaif ta ce mahaifinta Musulmi ne, mahaifiyarta Kiristal suna; da wurin ibada na Hindu

Bayan mun wallafa labari a shafukanmu na sada zumunta cewa jarumar finafinan Bollywood Katrina Kaif na cika shekara 39 da haihuwa, wadansu daga cikin masu bibiyar mu sun tafka muhawara a kan Musulma ce ita ko ba Musulma ba.

Don haka ne muka gudanar da dan gajeren bincike a intanet don gano addinin da Jaruma Katrina ke bi.

Da farko dai bincikenmu ya nuna cewa jarumar ba ta cika son yin bayani ba game da rayuwarta ta bayan fage idan tana hira da ’yan jarida.

Don haka babu magana tartibiya a kan addinin da Katrina ke bi a intanet.

‘Na yi imani da Allah’

Amma a wata hira da ta yi da mujallar India Today a watan Disamba a 2012, Katrina ta ce “Ni mai kakkarfan imani da Allah ce. A kullum nakan yi ‘addu’a’…”.

Kalmar da ta yi amfani da ita a harshen Ingilishi ita ce prayer, wadda za a iya fassarawa da addu’a ko sallah.

A wata hirar da jaridar Times of India ta watan Maris na 2015 kuma, Katrina ta ce ita mace mai addini – amma ba ta tantance addinin ba.

“Ko da yake mahaifina Musulmi ne mahaifiyata kuma Kirista, a gida an yi mana tarbiyyar bin dukkan addinai.

“A gidanmu akwai mandir (wurin ibada na mabiya addinin Hindu). Kuma ko da yake ba na yin pooja (ayyukan bauta) nakan kunna jyoti (fitilar bauta)”.

Wani abu da mai yiwuwa zai iya zama tabbaci ga waccan magana ta Katrina Kaif shi ne labarin da Times of India ta fitar ranar 11 ga watan Janairun 2018.

Jaridar ta ruwaito cewa a duk lokacin da za a saki fim din da ta fito a ciki, “ka’ida ce [jarumar] ta ziyarci Wurin Bautar [mabiya addinin Hindu na] Siddhivinayak, da Majami’ar Mount Mary, da kuma Hubbaren Ajmer Sharif [Hubbaren Sufi Moinuddin Chishti]”.

‘Mu muka kirkiro mata salsala’

Kamar yadda aka ji daga bakinta, jarumar ta ce mahaifinta, Mohammed Kaif, Musulmi ne dan asalin Kashmir wanda ke kasuwanci a Birtaniya amma yanzu yana zaune a Amurka, yayin da mahaifiyarta, Suzanne (ko Susanna) Turquotte, lauya kuma ma’aukaciyar agaji ’yar Ingila, Kirista ce.

Sai dai kuma akwai wadanda suke diga ayar tambaya a kan haka.

Misali, yayin wata hira da Mumbai Mirror, wacce ta shirya fim din da Katrina ta fara fitowa a cikinsa ta yi ikirarin cewa jarumar ba ta da wata alaka da Indiya.

A cewar Ayesha Shroff, “Mu ne muka kirkiro mata salsala. [Lokacin da ta zo] wata kyakkyawar Baturiya ce [wacce ba wanda ya san asalinta], saboda haka muka kirkiro mata mahaifi dan Kashmir.

“Da farko mun yi tunanin lakaba mata Katrina Kazi – tunaninmu shi ne sama mata salsala ta Indiya saboda ’yan kallo su ji cewa tasu ce…

“Amma sai muka ce Kazi suna ne da ya – shafi addini da yawa.

“A lokacin za mu gabatar da ita ga ’yan jarida kuma Mohammed Kaif na kan gaba [a jerin sunayen da muke tunanin lakaba mata] don haka muka ce, ‘Lallai Katrina Kaif ya yi sosai’”.

A cewar India Today, ba kasafai akan samu sunaye irin su Kaif a Kashmir ba.

A san mutum…

Hasali ma dai, a cewar Times of India, mutanen da suka san hakikanin wace ce Katrina Kaif ba su kai cikin cokali ba, don kuwa a cewar India Today, ba wanda ya san ta kafin zuwanta Indiya a 2002, lokacin da ko harshen Hindi ba ta fahimta.

Mai yiwuwa wannan na cikin abubuwan da suka sa ta kara haskaka a Bollywood.