✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bincike: Shin an kashe dan bindiga mai shan jini a Jibiya?

An taba kama kasurgumin dan bindiga Ibrahim Umar, wanda ya ce har jinin wadanda ya kashe yake lasa

An taba kama wani kasurgumin dan bindiga mai suna Ibrahim Umar, wanda ya shaida wa ’yan sanda cewa har jinin wadanda ya kashe yake lasa.

Ibrahim Umar wanda a wancan lokaci dubunsa ta cika a hanyar Kaduna zuwa Abuja ya ce yana lasar jinin wadanda ya kashe ne bisa ummarnin bokansa don kada ya haukace.

A wancan lokacin bidiyo da hotunan dan bindigar sun karade kafofin sada zumunta duba da yanayin shekarunsa da kuma irin rashin imaninsa. 

Sai dai kuma tun daga nan ba a sake jin duriyarsa ba, ballanta bayanin makomarsa.

Ce-ce-ku-ce a kan harin Jibiya

A makon nan ne aka yi ta yada wasu hotunan cewa an yi artabu da wasu ’yan bindiga a hanyar Jibiya zuwa Katsina.

A cikin hotunan har aka rika nuna gawarwakin ’yan bindigar da ake cewa an aika su lahira a artabun. 

Daga cikin gawarwakin har da na wani wanda ya yi kama da wancan Ibrahim Umar mai shan jini, wanda aka kama a kan hanyar Abuja a shekarun baya. 

Ganin wadannan hotuna ya sanya ce-ce-ku-ce da mahawara a tsakanin jama’a, musamman ma ganin fuskar dan bindigar. 

Wasu na cewa shi ne, wasu kuma na cewa a’a, yayin da wasu kuma ke tofin Allah tsine tare kuma da kara tabbatar da zargin da ake yi cewa ko da an kama ’yan ta’adda an gama shaidawa duniya, a karshe sai a rika ganin su suna yawo, an sake su ba kuma tare da shaida abin da ya faru ba.

Binciken kwakwaf

Sai dai binciken da Aminiya ta yi a kan labarin artabun da ya yi sanadiyar fitar da wadancan hotuna, ya gano cewa lamarin ba haka ba ne.

Aminiya ta kuma gano cewa babu wasu ’yan ta’adda da aka kama a hanyar ta Jibiya a lokacin da aka ayyana. 

Binciken namu ya tabbatar mana da cewa harin da ’yan bindiga suka kai a lokacin shi ne wanda suka tare motar sufuri ta Gwamnatin Jahar Katsina, inda kashe direban motar da wasu fasinjojin sannan suka tisa keyar wasu fasinjojin zuwa daji da nufin yin garkuwa da su domin karbar kudin fansa.

Shi ma yunkurin nasu bai yi nasara ba, domin bin sawunsu da jami’an tsaro suka yi, wanda ya sa tilas suka bar fasinjojin suka ranta a na kare.

Aminiya ta gano cewa a ranar Talatar nan da ta gabata ma ’yan bindiga sun kai wani hari da yunkurin tare a daidai inda suka tare a harin farko, garin Farun Bala.

 Amma nan ma hakarsu ba ta cim-ma ruwa ba, saboda isowar jami’an tsaron tun kafin su fara aiwatar da komia, wanda hakan ya sa suka tsere.

Wata majiya mai tushe daga ofishin Kungiyar Ma’aikatan Sufuri ta Kasa (NURTW) na garin Jibiyar ta shaida wa wakilinmu cewa, bayan tafiyar maharan daga wajen da suka fara tsayawa, “Ashe ba komawa suka yi inda suka fito ba.

“Sai suka zagaya suka sake komawa garin Kadobe inda suka taba kai hari har suka kashe jami’an shige da fice. 

“Nan ma rashin sa’a, ashe su ma jami’an tsaron da suka kore su daga wurin farko ba komowa baya suka yi ba, sun bi hanyar don ci gaba da yin sintirin da suka fito.

“A karshe dai wadannan ’yan bindiga tilas ta sanya suka koma inda suka fito,” a cewar majiyar.

Ta kuma tabbatar da cewa, babu wani harbi ko garkuwa da wani da aka yi a bisa hanyar domin, wakillansu da ke kauyukan da ke kan hanyar suna shaida musu abubuwan da ke faruwa.

A lokacin da muka tuntubi kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Katsina, SP Gambo Isa, kan batun ganin gawar Ibrahim Umar a cikin ’yan ta’addar da ake yadawa, ya ce, “Yadda kuka ji wannan haka muma muka ji, kuma muna nan muna bincike a kan batun.” 

Sai dai SP Gambo ya qara jan hankalin jama’a da su guji yada labaran kanzon kurege musamman a kafofin sadarwa na zamani. 

“Har in mutun yana da wani labari na sirri a kan sha’anin tsaro da sauran ayyukan laifi, mun bayar da lambobin jami’anmu da za a rika shaida wa, ba lallai sai an zo ofis dinmu ba.

“Amma maimakon yin hakan kawai sai mutun ya kirkiri labari ya kuma ci gaba da yada shi, wanda hakan barazana ce ga kowane irin sha’anin tsaro.

“Saboda haka, masu irin wannan dabi’ar yana da kyau su bari domin suna wasa da rayuwar al’umma da dukiyoyinsu,” inji SP Gambo Isa.