Daily Trust Aminiya - Binciken Magu: Malami ya ki amsa gayyatar kwamitin Salami
Subscribe

Ministan Shari’a Abubakar Malami

Binciken Magu: Malami ya ki amsa gayyatar kwamitin Salami

Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya ki bayyana gaban kwamitin Tsohon Shugaban Kotun Daukaka Kara, Ayo Salami, da ke bincikar dakataccen Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Ta’annati (EFCC), Ibrahim Magu.

Mai Shari’a Salami, ya gayyaci Malami ne domin bayar da shaida kan takardar zargin da ya rubuta wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, da ta haifar da nada kwamitin da ke bincikar Magu.

Gayyatar ta biyo bayan rokon da Magu ya yi wa kwamitin na a ba shi damar fuskantar wadanda suke zargin sa, ciki har da Ministan Shari’ar.

A cewar takardar gayyatar, “Ana umartar ka da sunan Shugaban Kasar Najeriya, ka bayyana gaban kwamitin bincike na shari’a domin bayar da shaida kan zargin da ka ke yi wa Ibrahim Magu”.

Maimakon ya bayyana, sai Malami ya rubuto wa kwamitin cewa ba zai bayyana a matsayin shaida ba, saboda takardar da ya rubuta na dauke ne da zarge-zargen wasu suka kawo masa ne a kan Magu.

Idan ba a manta ba, ministan, a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Arise ya sha alwashin amsa kiran kwamitin binciken a matsayinsa na Malami ko kuma Ministan Shari’a.

More Stories